HATSARIN MOTA: Rayuka 1,618 suka salwanta a cikin watanni uku

0

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa, ta ce akalla an yi asarar rayuka 1,618 sanadiyyar hadarin mota a kasar nan.

Ya ce wannan adadi na kididdigar hadurran da suka faru ne a cikin watanni uku kacal, daga Disamba 2018 zuwa Fabarairu, 2019.

Rahoton ka kuma kara nuni da cewa mutani 21,577 suka yi hadari a kananan motoci, bas-bas, babura, taraktoci, tankoki da tireloli a taskanin Disamba 2018 zuwa Fabrairu, 2019.

Hukumar FRSC ce ta fitar da wannan kidaiddigar.

Hukumar ta kuma bayyana cewa manyan dalilai biyar da ke haddasa hadurran sun hada gudun tsiya, wuce matar da ke gaban direba ba a lokacin da ya kamata ka wuce ta ba, tukin-ganganci, fashewar taya da kuma tsinkewar burki.

Sanarwar ta kara da cewa an fi yawan yin hadurra a kan titin Abuja zuwa Kaduna, kuma a can ne aka fi samun rahotannin salwantar rayuka da jin raunuka.

Akwai kuma titin Lagos zuwa Ibadan da Abuja zuwa Lokaja da kuma Kaduna zuwa Zariya cikinn titinan da aka fi yin hadarin motoci.

Rahoton ya yi kira da a karfafa wayar wa da direbobi kai da sauran masu motocin hawa da na sufuri domin a rage yawaitar wannan harudda.

Share.

game da Author