Haka zabe ya gada, ina taya Ahmed Lawal murna da yi masa fatan Alkhairi – Ali Ndume

0

Sanata Ali Ndume ya bayyanawa manema labarai bayan faduwa da yayi a zaben zama shugaban majalisar dattawa da yayi.

Ali Ndume ya yi takarar zama shuagaban majalisar dattawa inda ya fafata da Ahmed Lawan.

Sakamakon zaben da magatakardan majalisar tarayya ya bayyana bayan sanatoci sun kada kuri’un su, Ahmed Lawan ya samu kuri’u 79 inda shi kuma Ali Ndume ya samu kuri’u 28 kacal.

Bayan haka Magatakardan majalisar Tarayyan Sani Omolori ya rantsar da Ahmed Lawan tare da mataimakin sa Omo-Agege.

Ndume ya ce babban dalilin da ya sa ya dage sai yayi takarar shine don ya nuna wa duniya cewa jam’iyyar sa ta APC tabi yadda dokar kasa ta ke.

” Doka ta ce dole sai an gudanar da wadda a dalilin haka yasa na ce lallai dole sai an yi wannan zaben. Yanzu an yi kuma na samu kuri’u 28 kuma duniya ta gani cewa mun yi zabe. Kaga hakan da muka yi zai kara wa jam’iyyar mu ta APC daraja a idanun mutane da duniya.

” Tare da Ahmed Lawan muka yi zaman majalisar tarayya. A wancan lokacin nine shugaban jam’iyyar mu a majalisar, zuwa yanzu da muke majalisar Dattawa. Bani da matsala da shi. Muna zaman amana da shi. kuma ina mishi barka da murnar nasara da ya samu a zaben.

Share.

game da Author