HAJJIN BANA: Za a rufe karban kudin Hajji ranar 20 ga watan Yuni a jihar Kaduna

0

Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kaduna ta tsaida ranar 20 ga watan Yuni ranar da za a rufe aikin hajjin bana a jihar.

Kakakin hukumar Yunusa Abdullahi ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranan a Kaduna.

Ya ce hukumar ta tsaida da wannan rana ne domin ta iya tantance wadanda suka biya da kuma samun cika sharuddan da hukumar aikin Hajji ta kasa ta gindaya musu.

Takardar ya tabbatar da cewa duk maniyyacin da bai biya kudin tafiyarsa ba ko kuma bai kammala biyan kudin tafiya ba kafin wannan ranar 21 ga Yuni, toh fa sai dai ya hakura sai badi.

“Bana jihar Kaduna ta samu kujeru 6,636 wanda daga ciki mutane 3,000 ne kacal suka iya biyan kudin su ciff-cif zuwa yanzu.

Share.

game da Author