Gwamnatin Najeriya ta zargi mahaifiyar Leah Sharibu da kantara karya a Amurka

0

Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Washington, Amurka, ya nuna rashin jin dadin yadda a wurin wani taro a Amurka wasu da suka yi ikirarin hare-haren Boko Haram da rikicin makiyaya da manoma ya shafa suka yi karairayi a kan Gwamnatin Tarayya.

Taron wanda gangamin tattaunawa ne da wadanda aka ce rikice-rikicen suka shafa, an ba su fili kowa ya fito ya bada labarin abin da ya same shi.

Wata Cibiyar Gidauniya ce mai suna Heritage Foundation da ke birnin Washington ta shirya shi a ranar 11 Ga Yuni.

Wani babban jami’in ofishin jakadancin Najeriya ne mai suna Mohammed Suleiman ya sa wa takardar hannu, a madadin jakadan Najeriya a Amurka.

Sannan kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa an aika sakon tun a ranar 18 Ga Yuni aka aika da sanarwar.

Cikin wasikar, Najeriya ta zargi Heritage Foundation da dauko Rebecca Sharibu, mahaifiyar Leah Sharibu, Alheri Bawa Magaji da Napoleon Adamu, suka je suka rika kantara karairayi kan Najeriya, ba tare da sun tsaya sun yi kwakkwaran bincike ba.

Sannan kuma ofishin jakadancin ya nuna mamakin yadda gidauniya kamar Heritage Foundation, wadda ta shahara a duniya, amma za ta bari wasu mutane su je a gaban ta su na fadar abin da ba shi ba ne gaskiyar lamari.

“Dangane da haka ne ofishin jakadancin Naheriya na sanar da nuna rashin jin dadin sa da kuma neman Heritage Foundaion ya sake bai wa gwamnatin Najeriya dama ta zo ta yi bayanin yadda gaskiyar lamari ya ke.

“Sannan kuma a dauko wasu daga Najeriya su yi jawabai, wadanda ba za su nuna son kan su ba.”

Share.

game da Author