Gwamnatin Najeriya ta karyata zargin kuntata wa Kiristocin kasar nan, wanda Kungiyar Dattawan Kiristocin Arewa ta yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Wannan kakkausan martani da musanta zargi na dauke ne a cikin wata wasika da Babban Jakadan Najeriya da ke Birtaniya, George Oguntade ya aika wa wasu ’Yan Majalisar Birtaniya a jiya Alhamis.
Cikin wasikar, Gwamnatin Najeriya karya ce karara da rashin tunani har wani ko wata kungiya ta fito ta ce wai Boko Haram ajanda ce ta gwamnati ke amfani da ita a kan Kiristocin Najeriya.
Oguntade ya ce ya na ganin akwai muhimmancin ya fito ya yi musu karin haske sosai a kana bin da Najeriya ke ciki.
Oguntade, wanda tsohon mai shari’a ne a Kotun Kolin Najeriya, ya yi wannan martanin ne ga Ofishin Harkokin Wajen Birtaniya Mai Lura da Batutuwan Zargin Takura Wa Kiristoci a Kasashe Rainon Ingila.
Ya nuna cewa tabbatar da tsaron gwamnati da tsaron kasar Najeriya ya dogara ne wajen hadin kai ga al’ummar kasar nan baki daya daga kowane bangaren addinai.
Ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Kasa Kirista ne, kuma Shugaba Buhari kan yi taruka da shugabannin Kiristoci a ciki da wajen Najeriya a inda ya samu kan sa.
Sannan kuma ya ce ministocin Najeriya ma raba-daidai ake yi tsakanin Musulmai da Kiristoci, kuma shi kan sa Babban Jakadan, baya ga cewa Kirista ne, Babban Jagora ne ma a Darikar Kiristocin Angalika a Najeriya.
Ya kara da cewa shi kan sa Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya na yawan taruka da shugabannin Kiristoci da na Musulmai domin kara dankon zamantakewa a tsakanin juna.
Da ya juya kan wasu rikice-rikice da ake fama da su, Oguntade ya shaida cewa dukkan su ana fama da su ne tun kafi hawa mulkin Gwamnatin Shugaba Buhari, amma kuma ita wannan gwamnatin ta na ta kokarin kawo karshen su.
Discussion about this post