Gwamnatin Kano ta aika wa Sarkin Kano takardar neman dalilin facaka da naira bilyan 3.4

0

Gwamnatin Jihar Kano ta nemi Mai Martaba Sarkinn Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya bada ba’asin yadda Masarautar sa ta kashe kudi har naira bilyan 3.4.

Wasikar da aka aika ta nemi Sarki ya amsa wannan tuhuma a cikin kwanaki biyu rak.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Hukumar Hana Rashawa ta Jihar Kano ta zargi Masarautar Kano a karkashin Sarki Sanusi da yin facaka da naira bilyan 3.4.

A kan wannan dalili ne hukumar ta aika wa masarautar takardar tuhumar neman ba’asi.

An aika wa Sarki wannan takarda a yau Alhamis, wadda Sakataren Gwamnatin Jihar, Usman Alhaji ya sa wa hannu.

Jama’a da dama na ganin cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na takura wa Sarkin saboda bai goyi bayan sa ba a lokacin zaben 2019.

Ganduje ya ci zaben 2019 a karo na biyu bayan an yi zaben raba-gardama, saboda INEC ta ce na farko bai kammalu ba.
An kuma hakkake cewa an yi tashe-tashen hankula da kuma cin zarafin masu jefa kuri’a.

Hukumar Hana Rashawa ta Kano ta nemi a dakatar da Sarki.

Ganduje shi ne gwamnan da aka kama ya na boye milyoyin daloli a cikin aljihu. Sai dai wannan harkalla ba ta hana shi komawa a kan mulki ba.

PDP ta kai karar nasarar da INEC ta ce Ganduje ya yi.

Share.

game da Author