Gwamnatin Kaduna ta ce dole Masallacin ASD ya koma na Khamsa Salawat ba Jumma’ a ba

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta ki amincewa da aci gaba da sallan Juma’a a sabon masallacin da ASD ya gina a gidansa dake titin Yakubu Avenue Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta ce wannan gini ya saba dokar gini na jihar domin an gina abinda ba haka ba.

” Abin da aka ce za a gina a wannan gida shine masallaci yin sallah biyar, kawai sai masu ginin suka gina babban masallaci na Juma’a a wannan gida.

” Hukumar tsare-tsare na jihar Kaduna, KASUPDA tun a wancan lokaci sun rika yi wa masu iko da wannan gini tunin cewa wannan wuri bai dace a gina masallacin Juma’a ba kuma ma ba abin da aka ce za ayi ba kenan, amma suka yi musu kunnen uwar shegu.”

A makon da ya gabata ne aka kaddamar da masallacin inda aka yi sallah Juma’a na farko a wannan masallaci. Sai dai kuma ranar Juma’a da ta za gayo, sai aka hana sallah a wurin saboda karya doka da masu iko da wannan masallaci suka yi.

Duk da cewa jami’an ‘yan sanda sun halarci wannan wuri, basu hana kowa ya halartarci wannan wuri ba domin kuwa duk wanda yazo zai ga masallacin ne a rufe.

Da muka ziyarci wannan masallaci, mun ganshi a rufe babu kowa a wurin.

Sannan wasu da suke shawagi a wannan wuri sun bayyana wa wakilinmu cewa idan za ayi wa mutane adalci wannan wuri bai cancanta a yi masallacin juma’a a ciki ba domin cikin unguwa ne kuma babu filin da za ace wai juma a ke yi a ciki.

Yanzu dai gwamnati ta ce masu iko da wannan masallaci su gaggauta maida shi masallacin Khamsa salawatu ba na Juma’a ba domin abin da suka nemi a amince musu da shi ke nan.

Share.

game da Author