Gwamnatin jihar Neja za ta karo taraktoci 10 domin manoman jihar

0

Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa za ta kashe Naira biliyan 1.8 wajen siyo taraktoci 10 domin bunkasa aiyukkan noman bana a jihar.

Gwamnan jihar Abubakar Bello ya sanar da haka a taron kaddamar da siyar da takin zamani da aka yi a garin Minna.

Bello yace gwamnati ta hada gwiwa da kungiyoyi, masu ruwa da tsaki a fannin aiyukkan noma a jihar domin karo wadannan taraktoci.

Wadannan kungiyoyi sun hada da ‘Nigeria Incentive-Based Risk Sharing System for Agricultural Lending (NIRSAL),’ ‘Machine Equipment Consortiums Africa (MECA)’ da ‘Tractor Owners and Operators Association of Nigeria (TOOAN).’

Bayan haka Bello yace a damunan bana gwamnati za ta rage farashin kayan aikin noma domin tallafa wa manoma jihar.

“ A Duk damina gwamnati na samar da tallafi ga manoma ta hanyar sauwake musu kudin taki da iri da kuma maganin kwari da za su yi amfani da.

“ Bana gwamnati za ta siyar da kowani buhu na taki akan Naira 5,500 sannan ta tanadi isassu kuma ingantattun irin waken soya, shinkafa da dawa da maganin feshi domin kwari.

Bello ya ce gwamnati ta kammala shiri tsaf domin ganin an siyar wa manoma wadannan kayan aiki a farashi mafi sauki a duk kananan hukumomin jihar.

Babban sakataren ma’aikatar aiyukkan goma na jihar Ibrahim Musa ya yi kira ga manoma da su guje wa siyan jabun kayan aikin noma a kasuwanni.

Share.

game da Author