Gogarman satar Sandar Mulkin , Omo-Agege ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

0

Majalisar Dattawa ta zabi Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

Ya samu kuri’u 69, shi kuma abokin takarar sa, Sanata Ike Ekweremadu ya samu kuri’u 38.

Omo-Agege Sanata ne da ke wakiltar Shiyyar Jihar Delta ta Tsakiya.

Zaben na nuni da cewa dukkan sanatocin PDP sun zabi Ekweremadu kenan, su kuma na APC duk sun zabi Omo-Agege.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Jam’iyyar APC mai mulki ta tsaida Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin wanda ta ke so a zaba Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

Sannan kuma ta bayyana cewa Hon. Idris Wase daga Jihar Nassarawa a Matsayin Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.

Yayin da Omo-Agege ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan.

An rantsar da shi a daidai karfe 1:57 na rana, bayan kammala zaben Shugaban Dattawa, Lawan.

Jam’iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari duk sun goyi bayan a zabi Omo-Agege, gogarman da ya ja zugar satar Sandar Mulkin Majalisar Dattawa cikin 2018.

Omo-Agege shi ne gogarman da ya ja zugar wasu kartin matasa ’yan takife, suka kutsa Zauren Majlisar Dattawa, har suka sace Sandar Mulkin Majalisa.

Duk da cewa dai ya musanta wannan zargi, amma dai kwamitin bincike da Majalisar Dattawa ta kafa, ta same shi dumu-dumu da aikata wannan laifi.

Har ila yau, wani binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta gudanar a lokacin, ya tabbatar da cewa Omo-Agege dai ya dauko sojojin hayar wadannan matasa ‘yan Arufta, wadanda suka kutsa cikin majalisar har suka sace Sandar Mulki.

Duk da cewa an gano sandar mulkin daga baya, har yau babu ko mutum daya da aka gurfanar kotu ko aka hukunta dangane da wannan sata.

A wannan zabe na mataimaki, fafata ne tsakanin Sanata Ovie Omo-Agege na APC da kuma Sanata Ike Ekwaremadu na PDP.

Idan ba a manta ba, bayan satar Sandar Mulkin Majalisar Dattawa, sai da jami’an ‘yan sanda suka kama Sanata Ovie Omo-Agege, bayan hatsaniyar da magoya bayan sa suka tayar inda suka kutsa cikin zauren Majalisar Dattawa suka arce da Sandar Mulki.

An kama Sanatan ne a harabar Majalisar Tarayya inda aka fice da shi a cikin bakar mota kirar Totota Hilux da misalign karfe 1:54 na yammacin Larabar da rikicin ya faru a cikin 2018.

Share.

game da Author