Gobara ta lashe kayan tallafin ’yan gudun hijira a Barno

0

Da jijjifin safiyar yau Laraba ne gobara ta lashe kayyakin tallafin masu gudun hijira na milyoyin nairori, a wani babban rumbun ajiyar kayan agaji da ke kan titin Baga, cikin Maiduguri.

Rumbun ajiyar dai mallakar Kwamitin Rabon Kayan Agaji na Shugaban Kasa ne.

An ruwaito cewa wutar ta kama da misalin karfe 6 na fiyar yau Laraba, kuma ta cinye kimanin katifu 400, ta lashe wata mota da kuma kayyayaki masu tarin tarin yawa.

Jami’an Sintiri na NSCDC, ‘yan sanda, kwana-kwana da kuma makwabta sun garzaya wajen kai dauki domin taimakawa a kashe wutar.

Kakakin Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Barno, Ambursa Pindar, ya tabatar da tashin gobarar, tare da cewa jami’an su sun kai daukin gaggawa.

Ya ce gobarar ba ta ci rayuka ko daya ba, amma ta ci kayyaki da wata mota kirar Jeep da ta dade ajiye a wurin.

Har zuwa yanzu dai ba ta tantance musabbabin tashin gobarar ba, wadda ta ci kayayyakin.

Sannan kuma ba a kai ga tantance ainihin asarar kaya da kayan abincin da suka salwanta ba. Amma dai an kiyasta sun kai na milyoyin nairori, kamar yadda aka tabbatar.

Share.

game da Author