Gbajabiamila ya zama Kakakin Majalisar Tarayya

0

Tsohon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, ya zama sabon Kakakin Majalisar Tarayya.

Gbajabiamila ya samu kuri’u 281, shi kuma abokin takarar sa Umar Bago ya samu 76.

Bayan shafe sama da sa’o’i uku ana ana jefa kuri’a, Majatakardar Majalisar Tarayya, Mohammed Sani-Omolori ya bayyana sunan Gbajabiamila a matsayin sabon Shugaban Majalisar Tarayya.

Tun kafin a kai ga bayyana sunan sa majalisa ta kaure da sowa, da murna da tafi da yi wa Gbajabiamila murna.

Gbaja da shi da sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, su ne Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyyar APC ke goyon baya.

Dukkan majalisun guda biyu an gudanar da zaben su a yau Talata.

Da ya ke jawabi, sabon Kakakin Majalisar Tarayya ya godewa Shugaba Muhammdu Buhari da jam’iyyar sa da kuma mahaifiya da matar sa.

Ya ce iyalan sa sun yi juriyar rashin samun sukunin zama tare da shi har tsawon wata daya, inda ya rika rangadin neman zaben da ya karade jihohin kasar nan ya na neman goyon bayan mambobin majalisa da gwamnonin jihohi, musamman na jam’iyyar APC.

Ya kuma gode wa daukacin mambobin majalisa daga kowace jam’iyya baki daya.

Ya sha alwashin yin amfani da mukamin sa na majalisa wajen ganin an ciyar da kasar nan a gaba fiye da kowane ra’ayi ko muradin wani ko wasu.

Gbaja ya kuma nemi hadin kan dukkan mambobin na majalisar tarayya.

Share.

game da Author