FARFADIYA: Kashi 75 bisa 100 na mutanen dake dauke da ciwon na zama a kasashe masu tasowa ne – WHO

0

Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi ya nuna cewa kashi 75 bisa 100 na mutanen dake dauke da ciwon farfadiyya na zama ne a kasashe masu tasowa.

WHO ta ce samar da maganin ciwon a farashi mai sauki zai taimaka wajen ceto rayukan mutanen dake fama da shi a wadannan kasashe na duniya.

Idan ba a manta ba wasu likitoci da suka kware a wajen kula da masu fama da ciwon Farfadiyya a kasar Australia sun gano cewa ganyen Wiwi na warkar da masu fama da ciwon farfadiya.

Shugaban likitocin John Lawson ya bayyana haka sannan ya kara da cewa sun gano haka ne a wani bincike da suka gudanar a jikin wasu yara dake fama da wannan ciwo su 40.

” Da muka gwada yin amfani da ganyen a jikin yaran sai kusan rabi daga cikin su suka warke, sauran da basu warke ba amma sun sami saukin gaske daga ciwon.

Lawson ya ce duk da cewa binciken da suka yi a wancan lokaci ya samar musu da sakamako mai kyau, amma ci gaba da yin gwaji a akai domin samun nasara zai taimaka wajen samar da kula mai nagarta ga masu fama da ciwon.

Ya yi kira ga gwamnati da ta kafa matakan da za su hana iyaye da mutanen da suke fama da wannan ciwon yin amfani da ganyen wiwi kai tsaye domin yin haka na tattare da matsala.

Sannan ya kara yin kira ga gwamnatocin kasashe da su gaggauta sarrafa wannan maganin.

Ciwon Farfadiyya

Ciwon farfadiyya ciwo ne dakan shafi kwakwalwar mutum inda mai dauke da shi zai rika suma.

Malaman asibiti sun bayyana cewa akan gaji cutar, buguwa a kai na haddasa cutar, kamuwa da cututtuka kamar su Kanjamau, ciwon siga, cututtukan dake kama zuciya, bakon dauro da yawan firgita na kawo ciwon.

Malaman asibitin sun kuma bayyana cewa shan maganin hana suma, gujewa kamuwa da cututtuka, gujewa jin rauni a kai sannan cin abincin dake inganta garkuwa jiki musamman ga mai ciki na daga cikin matakan gujewa kamuwa da cutar.

Likitocin sun kuma ce a hanzarta zuwa asibiti idan mai dauke da cutar ya yi suman da ya fi tsawon mintuna biyar,idan wani suman ya faru bayan wani,idan mai dauke da cutar na da ciki, idan mai dauke da cutar na dauke da cutar siga.

Share.

game da Author