Kotun koli ta kori sanata David Umaru dake wakiltar Neja ta Gabas.
Kotun ta ce hukuncin kotun daukaka kara ta yanke cewa shi David Umaru dinne ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na Neja ta Arewa.
Kotun ta ce tun farko Muhammed Sani ne yayi nasara a zaben fidda gwanin saboda haka shine mai mallakin wannan kujera.
Kuma bisa ga hujjojin da aka bayyana a gaban kotu tun daga farko, ba David Umaru bane ya yayi nasara a zaben fidda gwanin.
Alkalan kotu da suka yanke hukuncin wanda maishari’a Ibrahim Mohammed ya jagoranta sun tabbatar wa Sani kujeran sannan sun umarci kotu da ta amshe Satifiket din da ta ba Umaru ta mika wa Mohammed Musa.