Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bbayyana cewa fadar gwamnatin Amurka wato ‘White House’ fa ta fada cikin dimuwa da hauka.
Rouhani ya bayyana haka ne a martani da ya maida wa gwamnatin Amurka din bisa takunkumin da ta kakaba wa jagoran kasar Ayatullah Khomenei da wasu manyan kasar.
Amurka fa ta sani cewa shiru-shiru ba tsoro bane amma kuma tana bukatan a je a duba kwakwalwan masu mulki a ksara domin akwai alaman zautuwa da hauka.
Idan ba a manta ba tun bayan kakkabu wani jirgin Amurka da kasar Iran ta yi aka fara takun saka mai tsanani tsakanin kasashen biyu.
Kasar Iran ta ce wannan jirgi shine ya shigo mata sarararin samaniya babu sallama, ita kuma ta mako shi.
Amurka ta ce inda ta bi bai shiga samaniyar kasar Iran din ba.
Daga nan sai Amurka din ta yi shirin kai wa Iran hari a sansanonin da take girke makamanta. Sai dai kuma ana gab da za afara yi wa Iran luguden bama-bamai sai shugaba Donald Trump na ya ba da umarnin a dakatar da kai wannan hari.
Sabbin takunkumin da aka kakaba wa kasar Iran din sun hada da daga yanzu da jagoran kasar, Khomenei da wasu manyan kasar ba za su samu daman amfani da wani kudi a wani asusun banki da kasar Amurka ke da iko da shi ba a duniya.
Rouhani ya ce wannan maganar banza ne domin Khomenei ma bashi da asusun ajiya a wani bankin kasar waje.
Discussion about this post