El-Rufai yayi sabbin nade-nade

0

Gwamnnan jihar Kaduna ya maido da kakakin gwamnatin jihar Samuel Aruwan da wasu masu taimaka masa kan mukaman su.

Sakataren gwamnan El-Rufai, Salisu Suleiman ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Samuel Aruwan wanda sanannen suna ne musamman ga mutanen jihar Kaduna wajen zakewar da yake yi na kare ubangidan sa wato gwamna El-Rufai na daga cikin jerin wadanda aka nada.

Ga sunayen wadanda aka nada:

1 – Maryam Abubakar, Babban mai taimakawa wa gwamnan El-Rufai kan sabbin kafafen yada Labarai.

2 – Saude Amina Atoyebi, Babban mai taimakawa gwamnan kan Ayyuka.

3. Mukhtar Maigamo​​, Mai taimakawa wa gwamna kan hulda da jama’a

4. Manasseh Istifanu, Mai taimakawa gwamna kan harkokin yada Labarai.

4. Nuhu John Gwamna, Mai daukan hoto na musamman.

Share.

game da Author