Dole sai mutane sun hada hannu da gwamnati domin samun nasarar kauda Kanjamau a Najeriya – Stuart Syminton

0

Jakadan Kasar Amurka a Najeriya Stuart Syminton ya yi kira ga mutanen Najeriyada su hada hannu da gwamnati domin samun nasarar kawar da cutar Kanjamau a Najeriya.

Syminton ya yi wannan kira ne a taron karrama mutanen da suka tallafa wa ‘PEPFAR’ wajen samun nasarar hana yaduwar cutar kanjamau da aka yi a Abuja.

Ya ce ya yi wannan kira ne ganin cewa samun nasaran kawar da kanjamau a Najeriya ya dogara ne ga irin goyan bayan da mutanen kasar suke bada wa maimakon a bari wa gwamnati kadai.

Syminton ya kuma yi kira ga mutane da su rika yin gwaji domin sanin matsayinsu.

Bayan haka babban sakataren ma’aikatan kiwon lafiya Abdullahi Abdulazizi ya bayyana cewa domin kare jarirai daga kamuwa da kanjamau gwamnati ta yi nasaran yi wa mata masu ciki miliyan 1.6 gwajin cutar kyauta.

Abdulaziz yace gwamnati na bai wa yara kanana da marayu dake dauke da cutar magunguna kyauta a kasarnan.

Ya kuma ce ma’aikatar kiwon lafiya na kokarin samar da magungunan cutar a jihohi bakwai dake fama da karancin magungunan.

Wadannan jihohi kuwa sun hada da Ribas, Akwa-Ibom, Anambar, Delta, Legas, Imo da Enugu.

Abdulaziz yace ma’aikatar su ta gano wadannan jihohi ne a dalilin bayanan sakamakon binciken da akayi na sanin adadin yawan mutanen dake dauke da kanjamau da hukumar hana yaduwar cutar ta kasa (NACA) da NAIIS suka gudanar.

” Idan ba a manta ba a kwanakin baya hukumar NACA da NAIIS sun gudanar da bincike domin sanin adadin yawan mutanen dake dauke da kanjamau a kasar nan.

” Sakamakon ya nuna cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar a Najeriya inda daga ciki kashi 1.4 masu shekaru 15 zuwa 49, kashi 1.9 mata sannan kashi 0.9 maza.

” Binciken ya kuma nuna cewa yankin kudu maso kudancin kasar nan ne suka fi yawan mutanen dake dauke da cutar a Najeriya.

SABUWAN MAGANIN KANJAMAU

Jami’in hukumar USAID Babatunji Odelola ya bayyana cewa fannin sarrafa magunguna na USAID ya gano sabuwar maganin kanjamau mai suna TLD.

Odelola ya ce maganin TLD magani ne dake rage adadin yawan kwayoyin Kanjamau a jikin mutun a cikin lokaci kalilan.

Ya ce hakan na nuna cewa mai amfani da wannan maganin yadda ya kamata zai rage kwayoyin cutar a jikinsa cikin lokaci kalilan sannan maganin na da ingancin hana mutane yada cutar.

A karshe Odelola ya ce Najeriya na cikin kasashen duniyan da za su fara amfani da wannan magani.

Share.

game da Author