Jami’in hukumar gudanar da bincike kan magunguna ta kasa (NIPRD) Obi Adigwe yace abin takaici ne yadda hukumar ta kagara ci gaba duk da dunbin ilimin bokon da ake tunkaho dashi a kasar nan.
Adigwe ya fadi haka ne a taron samar da madafa kan rashin ci gaba da hukumar ke fama da shi wanda aka yi a babbar birnin tarayya Abuja.
Adigwe ya ce kamata ya yi yadda ake da yawa a kasar nan hukumar NIPRD ta iya sarrafa magungunan da zai amfani mutanen kasar nan a fannin inganta kiwon lafiya da tattalin arzikin kasan.
” Sai dai haka ba shine ke faruwa ba a kasar domin rashin ci gaba a fannin ya sa masana’antun mu na sarrafa magungunan basu da tasiri musamman idan suka zo jiki da jiki da ‘yan uwan su na kasashen waje.
Adigwe yace mafita shine idan hukumar ta hada hannu da fannin ilimi da aiyukkan noma domin bunkasa ayyukanta.