(GARGADI: Idan ka san ba ka da dakakkar zuciyar da za ta iya jure jin yadda wani ya samu kan sa cikin irin wannan mummunan hali, to kada ma ka karanta).
Wannan mummunan al’amari ya faru ne a ranar Juma’a, wajen karfe 3:30 na rana. Na tashi ni da direba na daga garin Ikare da ke cikin Jihar Ondo za mu tafi wani gari. Mu ka bi ta Ipele, ga mu nan sai Kabba, wato garin nan da ke cikin Jihar Kogi. Mu na kan babbar hanya, sai katsam muka riski wasu mutane a kan hanya. A tunani na mahara ne dai kawai ko kuma ’yan fashi da makami.
Wuce nan, ashe gaba da gaban ta! Abin da ya same ni ya faru kilomita 38 kafin Kabba, alhali kuma akwai shingen ‘yan sanda kilomita 42 kafin Kabba.
YADDA SUKA YI MANA KWANTON-BAUNA
Da ya ke ba ni ke tuki ba, ido na ya hange min wani matashi mai ruwan Bafulatani tsaye a gefen titi, ba aikin gona ko kiwo ya ke yi ba. Ya fi kama da mai yawon gallafiri.
Wuce shi ke da wuya sai mu ka ji karar harbin bindiga na farko. A lokacin kuwa akwai motoci da yawa a kan titin, a hannun tafiya da hannun dawowa duka. A gaban mu wata mota ce kirar Avensis. Yayin da direba na ya cimma motar, sai kuma na hangi wani Bafulatani dauke da bindiga, amma irin ta gargajiya din nan.
Daga nan sai na ji a jiki na lallai Bafulatanin da na fara gani daga farko a can baya, ya na daya daga cikin ‘yan bindigar da ke kokarin kawo mana hari kenan. Cikin kiftawar ido sai suka rika bayyana. Na dan leka ta madubin mota, sai na ga wasu da dama sun biyo motar mu a guje dauke da bindigogi, kowanen su ya na harbin-kan-mai-uwa-da-wabi.
Nan dai suka harbi tayar motar mu, mota kuwa ta fara wulle-wulle a kan Kidnapped victims, har dai ta kwace daga hannun direba, ta rika wuntsilawa da mu a ciki.
Bayann mota ta tsaya a rigingine, mu ka yi kokari muka fice daga ciki, mu na jan-ciki har muka shiga daji domin neman tsere wa maharan nan.
Duk abin nan mu fa dauka muka yi ‘yan fashi da makami ne kawai, wadanda idan suka karaso suka samu motar mu, to za su kwashi abin da suke so a ciki kawai su yi gaba.
Mu na cikin mirginawa daji, sai na waiwaya na hango Fulanin nan dauke da bindigogi, sun dumfaro mu su na ta harbi. A haka mu ka rika sauri don kada su cim mana.
Can dai na ce wa direba na kowa ya kama gaban sa, domin ko da sun kama daya, to idan daya ya tsira, zai iya bada labarin abin da ya faru da dayan idan ya isa gida. Ina cikin haka sai na ga kamar kato 11 sun kwaye ni, kowa rike da bindiga!
AN YI GARKUWA DA NI
Bayan sun kama ni, sun yi garkuwa da ni, sun kuma kama wasu daga cikin motar nan kirar Toyota Avensis. A cikin motar akwai maza biyu, sai kuma wata mace da ‘ya’yan ta biyu. Sai suka dauki mijin ta da dan’uwan sa. Mu uku kenan suka tarkata, suka nausa da mu a cikin daji.
Washegari ranar Asabar suka nuna mana gawarwakin wasu da suka kama, suka ce mana idan ba a biya su kudi ba, to mu din ma kashe mu za su yi kawai. Ni dai da ido na, na ga gawarwaki biyar a wurare daban-daban. Duk bayan awa 3 zuwa 4, muka dan tsaya mu buga waya. Su na barin mu kira ‘yan uwa mu sanar da su batun kai kudin diyyar fansar mu.
Su kuma sukan dauki wayoyin su su na kiran ogogin su. Amma dai idan za su yi magana da abokan mu ko ‘yan uwan mu, da wayoyin mu su ke yi ba da wayoyin su ba.
A ranar da suka kama mu, wato Juma’a din nan, sai da muka shafe kilomita 42 a cikin daji, kamar yadda agogo na ya nuna min, domin ya na da wata na’ura mai tantance irin wannan zangon tafiyar.
SU WA SUKA YI GARKUWA DA MU?
Maganar gaskiya zan iya shaida muku cewa su kan su wadanda suka yi garkuwa da mu din, a cikin tsoro suke. Na gano cewa duk da su din ma dai Fulani ne, to amma ba irin makiyayan da muka sani ba ne, domin su kan su na cike da tsoron Fulani makiyayan.
Sun shaida mana cewa su na fama da rikici da su. Daga daga cikin su ya shaida min cewa a baya su ka satar shanu, shi ya sa suke tsoron haduwa da makiyaya. A tsawon lokacin da na dauka a tsare, na rika hira da daya daga cikin su, saboda shi ya na jin Hausa sosai, ba kamar sauran ba.
Ta hanyar wannan mai jin Hausar na kara fahimtar yadda suke gudanar da al’amurran su. Idan suka ga Fulani makiyaya sun gabato mu, sai su karkada mu gaba su ce mu haye bishiyoyi ko tsaunuka mu boye, domin idan suka hadu da mu, duk kashe mu za su yi.
Na fahimci cewa Fulani masu garkuwa da mutane ba Fulani makiyaya shanu da mu ke gani ba ne. Su wadannan masu garkuwa din ko shanu ba su da su, kuma su na tsoron haduwa da Fulani masu kiwon shanu, domin za su gane cewa su k eke satar musu dabbobi.
Wanda mu ke yawan hira din nan ya ce min sun sha zuwa tafka ayyukan ta’asa a garuruwa daban-daban. Ya ce min har daukar su haya ake yi su je su yi kashe-kashe wasu wurare su dawo. Kamar yadda ya ba ni labari, da su aka yi fadan Benuwae, Nasarawa da Taraba. Kuma ya ce min wasu abokan aikin su biyu sun dawo daga Zamfara, inda suka je suka yi barna suka dawo.
Babban abin mamaki shi ne wadannan masu garkuwa duk su na aiki ne a karkashin wani ya na biyan su. Lokaci kadan za mu ga sun buga masa waya, ko kuma ya bugo masu. Akwai ma lokacin da suka tambaye shi ko su kashe ni ne kawai? Amma sai na ji ya ce a’a, kada su yi saurin kashe ni.
BA SU DA TAUSAYI KO NA SISIN KWABO
Wadanda suka yi garkuwa da mu ba su da tausayi ko na sisin kwabo. Akwai ranar da wata Lahadi da daya daga cikin su ya hango Fulani makiyaya tafe, sai ya kidime, ya bazama ya dauko wasu kayan tsibbace-tsibbacen sa ya fara yin surkulle a gaban mu. Wato ya fara shirin fada kenan.
Amma da ba a yi fadan ba, sai jikin sa ya kasa daina karkarwa, ya yi ta cika ya na batsewa ya na fagamniya. Sai ya fara hargagi, ya na cewa idan fa bai kashe mutum ba , to hankalin sa ba zai dawo jikin sa ba.
Sai da aka shafe sama da awa uku abokan sa na lallashin sa kafin ya dan natsu. A karshe dai sai da suka kawo masa biri ya kashe, ya sha jinin sa, sauran jin kuma ya yi wanka da shi tukunna.
Gaskiya wadannan mutane ba zan kira su mutane ba. Ogan su ya shaida min cewa ya kai shekara goma kenan ya na wanann mummunar harka.
BATUN ABINCI
Gas hi dai cikin watan azumi ne, amma sun hana ni yin azumi. A ranar Juma’ar da suka kama mu, sun bar ni na yi sallah, kuma na kai azumi wanda na ke dauke da shi a ranar. Amma washegari Asabar ba su bar ni na yi azumi ko sallah ba.
Har aka ceto mu ranar Litinin ba su bar ni na yi sallah ko azumi ba. Ce min suka yi idan na yi sallah, asiri da lakanin su karyewa zai yi.
Garin rogo suke ba mu m na ci. Shi din ma, garzagon garin suke ba mu, ba jikakke ko wanda aka tuka ba. Sai su ba mu ruwa wanda suke debo daga tafki ko korama su ba mu mu sha. Amma sun taba dafa mana shinkafa sau daya. Ita ma garau-garau, farar ta, ba mai ba miya.
YADDA MUKA TUBUTA
Mun biya adadin kudin da suka nema a biya kafin a sake mu. Ni dai na biya naira milyan 1.8, sauran wadanda aka kama mu tare kuma kowanen su ya biya naira milyan daya. Kenan gaba daya mun biya naira milyan 3.8. Sun shaida min cewa sun ma taba kashe wani dan kasar waje mai aiki a kamfanin wanda suka taba kamawa. Sun tilasta na biya kudi da yawa, saboda ina aiki a kamfanin da suka ce sun san shi.
Sun sake mu ranar Litinin da yamma bayan sun karbi kudin fansa. Suka tambayi inda na ke zaune, na ce musu a Lokoja. Sauran kuma suka ce a Okene.
NA CI DUKAN TSIYA
Kafin su sake ni sai da na ci dukan tsiya. Sun rika gabza ta da gindin bindiga. Bayan na je gida sai da na je asibiti aka ba ni magunguna, sannan likita ya ce min na koma bayan kwana bakwai. Na ci dukan tsiya don saboda sun ga na yi magana da sauran mutane biyun da aka tsare mu tare.
Daya daga cikin su ne ya shiga garari matuka, har muka rika lallashin sa. Wannan ne ya harzuka su, suka rika gabza ta kafin su sallame mu.
Jama’a, suna na Ibrahim Lawal. Wannan shi ne labarin abin da ya faru da ni a hannun wadanda suka yi garkuwa da ni.