Jaridar PREMIUM TIMES ta samu yin wannan mashahuriyar tattaunawa da Mohammed Bello Adoke, Ministan Shari’a na lokacin mulkin Goodluck Jonathan, daga 2010 zuwa 2015, a Accra, babban birnin kasar Ghana. Wannan tsakure ne daga cikin hirar da aka yi da shi, domin masu karatun mu su karanta su ji irin kwatakwangwamar tuggu, kutinguila da annamimancin da manyan jami’an gwamnati su ka sha tafkawa a lokacin gwamnatin Jonathan, musamnan kafin saukar sa.
Ku biyo mu ku ji asarkala da sabarkalar da ke tsakanin Tsohon da sauran rigingimun da ko ruwan Kogin Kwara da Kogin Neja ba za su iya kashe wannan tarangahuma ba.
DALININ FICEWAR ADOKE DAGA NAJERIYA
“Rade-radi da ikirarin da wasu ke ta yi cewa na gudu bayan zaben 2015, ba gaskiya ba ne. Dama can ina da shirin bayan kammala wa’adi na a matsayin Ministan Shari’a daga 2010 zuwa 2015, zan fita waje domin yin karin karatu. Na yi niyyar zuwa Jami’ar Georgetown da ke Washington. To amma sai wasu abokai da abokan aiki suka canja min shawara. Daga nan na shiga Jami’ar Leiden. Dalili kenan mu na kammala mika mulki, tunda ba mu yi nasara ba, sai na yi haramar fita waje na koma koma makaranta.
“Ko da jam’iyyar mu, PDP ta sake yin nasara, ni dai na rigaya na yanke shawarar tafiya karatu. Sai fa idan Shugaban Kasa ya jajajirce ya ce tilas na zauna na ci gaba da aikin bauta wa kasa ta Najeriya.
ABIN DA YA HANA ADOKE DAWOWA NAJERIYA
“Tabbas na kammala karatu na tun cikin Agusta, 2016. Da farko na yi niyyar komawa Najeriya, amma kun dai sani ina da matsala ko sabani da gwamnatin Najeriya mai ci a yanzu. An yi ta sheka ruwan zargi nan a gaskiya da kage da karairayi a kai na.
To sai na rika samun kwararan bayanai na sirri daga cikin manyan gwamnati da na wajen gwamnati, suka rika ba ni shawara cewa kada na koma Najeriya. Daga nan sai kawai na zarce ci gaba da karatun digirin-digirgir.
“Duk da haka dai, ba wai gudu na ke yi ba, kuma ba cewa na yi ba zan koma Najeriya ba, zan koma ko don na wanke kaina daga zargin da ake yi min. Magana ta gaba kuma ita ce ina fama da wata lalurar rashin lafiya. Ba zan koma ba, har sai na samu lafiya, na ji ni garau, yadda zan iya fuskantar tuhuma da shari’ar da za a yi min.
RAYUWAR ADOKE A MATSAYIN DAN GUDUN HIJIRA
“Gaskiya irin wannan rayuwa akwai wahala da kunci. Amma ina tare da kuma ina samun masu dawainiya da ni bakin gwargwadon iyawar su. Na kuma gode wa Allah da na same su. Amma irin wannan rayuwar tabbas akwai wahala da takura. Wasu mutane uku ne ke taimako na har ba na tagayyara.
Sai dai kuma ba zan bayyana sunan su ba. saboda wasun su su na cikin wannan gwamnatin tsundun. Akwai ma wani hamshakin da ya rika taimako na, har sai da wasu mutane suka yi masa barazanar cewa za su fallasa shi, domin sun gano ya na taimako na, har ina samun karfin-halin yin sa-in-sa da gwamnati.
BAN FICE DAUKE NA MAKUDAN KUDADE BA
“Don ina ma’aikacin gwamnati ko don na yi minista, ai ba aikin tara kudi na ke yi ba. A ina zan samu kudin? Akwai wani fili da aka ba ni, kuma shi na saida domin na ci gaba da irin rayuwar da na saba. Amma tsohon Ministan Abuja, Bala Mohammed bait aba ban i fili da suna na ko da sunan wani ba.
A duk lokacin da na shiga fatara, zan dauki fili na saida. Saboda haka kada ku yi tunanin wai a matsiyaci na na shiga gwamnati. Na shiga gwamnati ina da rufin asiri na bakin gwargwado, domin ina harkoki na.
Har na bar ofis ban ma yi amfani da motocin gwamnati ba, da nawa motocin na yi amfani.
‘DUK WANDA YA TABA BA NI CIN HANCI YA FITO YA TONA NI’
“Ni dai ma’aikata ta ba ta bayar da kwangila, kuma tambayar da ku ka yin ko ina karbar cin hanci da rashawa daga kwangiloli, to ina kalubalantar duk wanda ya taba ba ni, ya fito ya tona min asiri. Idan batun shari’a ya zo a gaban mu kuma ai ba ni ne sukutum ke bin ba’asin ba, wasu lauyiin mu na ke sawa su yi. Ina tabbatar muku har ga Allah cewa babu wani lauya da ya taba ba ni kudi na karba.
YADDA PATIENCE JONATHAN TA SURFA MIN ZAGI
“Gaskiyar magana tabbas Patience Jonathan ta surfa min zagi, saboda na taka rawa sosai wajen kokarin lallashin Goodluck Jonathan da kwantar masa da hankali cewa ya karbi kaddarar faduwa zabe, tun ma kafin a bayyana sakamako. Saboda mun hango abin da zai iya biyo baya, idan aka samu akasin haka. Ba ni kadai ba ne, don haka babu wanda zai bugin kirji ya ce ya fi wani taka rawa wajen bai wa Jonathan shawarar ya karbi kaddara.
“Ranar 30 Ga Maris, 2015, kwana daya kafin Jonathan ya mika wuyan karbar kaddara ne abin ya faru tsakani na da Patience. Amma a gaskiya ni dai ban ga laifin ta ba, domin ta fito ta amayar da bin da ke cikin zuciyar ta. Kenan ta fi sauran munafukan da suka rika zuwa su na cewa Jonathan wai ni Ministan Shari’ar sa ba na tare da shi.
Munafukai suka rika ce masa wai ni yaron Buhari ne, ina taimaka wa kamfen di Buhari da kudi. To sai ga shi su wadannan munafukan su ne ma suka kewayawa su na taimaka wa Buhari da kudin kamfen, alhalin kuma su na tare da Jonathan, a cikin gwamnatin sa.
Tabbas Patience ta surfa min zagi, amma dalili, a tunanin ta waccan mawuyacinn hali da ake ciki, sun dauka Ministan Shari’a, kuma Antoni Janar na Kasa, wato ni kenan, kamar rayuwar su ko mutuwar ta na ga hannu na. ita ba ta san ni kai na akwai iyakar hurumin da doka ta gindaya min ba. Patience ta surfa min zagi ne a bisa hujjar karairayin da wasu munafukai suka rika zuwa suna sheka mata dangane da ni.
“Ta kira ni shashasha wanda bai san abin da ya ke yi ba. amma fa ku tuna, ai ba shugaban kasa ne ya kira ni haka ba. Na same shi na ce ‘Ranka ya dade kai ka yarda ni sakarai ne kuma shashasha? Kuma ka yarda da abin da ake zuwa ana fada maka dangane da ni? Y a ce a’a bai yarda ba.
“To amma ku fa yi la’akari, ita mace ce, kuma matar shugaban kasa. Babu yadda za a yi ta so mulki ya subuce daga hannun su haka kawai. Maganar gaskiya kenan, shi ya sa ni ban rike ta a zuciya ta ba.
TSAKANI NA BOLA TINUBU
“Da ake cewa bayan an gurfanar da Bola Tinubu a kotun CCB, za a rika bi ana kama wasu ‘yan adawa a lokacin ana gurfanarwa, ciki har da Buhari, ba gaskiya ba ne. Na gajarce muku labari, wani lauya ne ma dan rajin kare hakkin jama’a ya ruruta wutar gurfanar da Tinubu Kotu.
Wannan lauya ne ya rika cewa, ‘yanzu kuna ganin yadda Tinubu ya sace kudadin Jihar Lagos, kuma za ku bari su sake kafa gwamnati a Najeriya, ya sace kudaden Najeriya? A haka za ku zura idanu Najeriya ta koma hannun Tinubu dan kakuduba? Daga nan ne mutanen CCB suka tuhume shi. Allah ya sa akwai wani lauya na nan da rai, ya san komai.
“Wancan lauya ne dai da ya je ya zuga CCB suka dirar wa Tinubu, kuma shi ne ya zagaye ya rika ce wa Tinubu ni ne ke son ganin bayan sa.
Sai bayan shekara daya wani lauya daga CCB ya zo ya same ni ya ce ya na so su sake bin ba’asin shari’ar Tinubu, akwai inda suka yi kuskure. Amma yanzu sun gano yadda za a daure shi. Na ce masa a’a, ba mu yin amfani da shari’a domin huce-haushin wani.
ALLAH YA ISA TSAKANI NA DA WANDA YA CE DA NI AKA KITSA TSIGE AYO SALAMI
Daga cikin wuraren da ’yan Najeriya ba su yi min adalci, akwai batun zargin da ake yi min wai ni ne na bai wa Goodluck Jonathan ya cire Cif Jojin Tarayya, Ayo Salami. Kai, na fi jin haushin wannan zargin fiye da kowane. Domin ba zan taba yafe wa wadanda suka yi min wannan sharrin ni da Jonathan ba.
Rigimar Ayo Salami ta su ce ta cikin bangaren shari’a. Salami ya zargi Mai Shari’a Katsina Alu, amma kwamiti ya gano duk abinda aka fadi dangane da Katsina-Alu, babu gaskiya a ciki. Aka nemi Ayo Salami yaba shi hakurin kazafin da ya yi masa, amma ya yi biris, ya yi mirsisi.
Duk mai wata tantanma ko tababa ya koma baya ya karanta abin da dokar Najeriya ta ce dangane da irin wannan katankatana.
Sannan kuma ya kamata jama’a su sani Salami da Katsina-Alu ‘yan aji daya ne a makaranta, akwai jikakka can ta su da ta taba hado su, amma dai ni ko ni da wasu babu ruwan mu, kuma babu ruwa na da rikicin su. Domin babu wata ribar da na ci ko da zan ci a rigimar ta su.