Dalilin soke Hawan Nasarawa – Ganduje

0

Gwaman jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa rade-radin yiwuwar tashin hankali ne yasa gwamnati ta soke hawan Nasarawa da ya kamata a ce yau ne akayi shi a Kano.

Idan ba a manta ba gwamna Ganduje basu ga maciji da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi tun bayan zaben 2019.

Rahotanni sun nuna cewa gwamna ya fusata ne tun bayan zargin sarki da yayi na yi masa zagon kasa a zaben da yayi nasara da kyar a Kano.

Bayan haka sai gwamna Ganduje ya fara da kirkiro sabbin masarautu a jihar har guda hudu kuma aka fara bincikar yadda masarautar Sanusi ta kashe kudadenta.

A rahoton binciken, an nemi gwamna da ya dakatar da sarki Sanusi daga kujerar domin ci gaba da binciken.

Sai dai kuma kakakin gwamnan Awwal Anwar ya bayyana cewa sarki ya soke hawan ne saboda wasu dalilai da ya hada da rashin tsaro.

A dalilin haka sarki ya ga ya dace a soke wannan hawa.

Share.

game da Author