Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta bayyana cewa rashin kwararrun ma’aikata, rashin samar da ingantattun kayan aiki a asibitoci musamman a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na daga cikin matsalolin dake hana Nahiyar Afrika iya kawo karshen yawan mace-macen yara kananan da mata a kasashen su.
Sakamakon binciken ya nuna cewa daga 1999 zuwa 2015 an samu raguwar kashi 43 daga cikin 100 na yawan mace-macen yara kanana da mata. Duk da haka binciken ya nuna cewa akwai sauran aiki a gaban kasashen nahiyar.
A 1999 adadin yawan yara da mata da suka mutu sun kai 532,000 amma a 2015 adadin yawan ya ragu zuwa 303,000.
KARANCIN MA’AIKATA
Bisa ga tsarin samar da ingantaccen kiwon lafiya ta 2017 da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta tsara, kamata ya yi kasashen Afrika na da likitoci, ungozoma da ma’aikatan jinya da suka kai miliyan 5.6 amma kuma miliyan 3.7 ne kawai ake dasu a nahiyar.
KARANCIN MA’AIKATA A NAJERIYA
Sakamakon binciken ya nuna cewa rashin yawan ma’aikatan kiwon lafiya a Najeriya ya yi wa fannin kiwon lafiyar kasar Najeriya katutu inda a duk shekara mata 576 da yara kananan ‘yan kasa da shekara biyar 37 ne ke mutuwa.
Sakamakon ya kuma nuna cewa an fi samun mafi yawan mace-macen yara kanana da mata a yankin arewacin kasar a dalilin fama da matsanancin talauci da suke yi.
Bayan haka kungiyar likitocin hakora na kasa (MDCN) ta bayyana cewa adadin yawan likitocin da suka yi rajista da kungiyar su a 2017 sun kai 42,845 wanda daga ciki 39,912 ne suke kwararru.
A lisaffe bisa ga hukumar kidaya ta kasa adadin yawan mutanen Najeriya a 2016 sun kai miliyan 193.4 sannan idan aka kwatanta yawan da yawan likitocin dake kasar nan za a gane cewa likita daya na duba akalla marasa lafiya 4,845 a Najeriya.
A karshe UNICEF ta yi kira ga gwamnatin Najeriya kan yin amfani da wannan sakamakon bincike wajen samar da mafita daga wannan matsala da ake fama da.
Haka na nufin daukar ma’aikata da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya.
Discussion about this post