CIWON SIKILA: Yin gwajin jini kafin ayi aure shine mafita ga ma’aurata – Likitoci

0

Ranar 19 ga watan Yuni na kowace shekara ne kungiyoyin duniya suka kebe domin wayar da kan mutane game da ciwon sikila.

Malaman kiwon lafiya sun bayyana cewa ana gadon cutar da hakan ya sa lallai idan mutane za su yi aure su tabbata sun yi gwaji.

Alamun ciwon sun hada da kumburin kafa da hannu, ciwon ido, kamuwa da cututtuka kamar su hawan jini, shanyewar bangaren jiki da sauran su.

ABIN DA BINCIKE YA NUNA

Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa akan haifi yara sama da 300,000 a duniya dauke da wannan ciwo.

Sannan kuma kashi 75 bisa 100 daga cikin wadannan yara daga kudu da Saharan Afrika suke, kashi 66 bisa 100 kuma daga Najeriya ake samun su.

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar Amurka (CDC) ta bayyana cewa akalla kashi 24 bisa 100 na mutanen Najeriya na dauke da wannan ciwo.

Sannan a duk jarirai 1,000 da ake haihuwa kashi 20 bisa 100 daga cikinsu na dauke da ciwon a kasar nan.

Rashin yin gwajin jini, rashin sani musamman a yankunan karkara na daga cikin matsalolin dake sa ciwon na ci gaba da yaduwa musamman a Najeriya.

A 2017 gwamnati ta kafa dokar tilasta wa ma’aurata da masu niyyar aure yin gwajin jinin su kafin su fara haihuwa.

Kafa wannan doka na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin hana yaduwar cutar. Sai dai har yanzu wannan doka bai fara aiki ba a kasar.

A kwanakin baya kuma tsohon ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta fara sarrafa maganin cutar sikila mai suna ‘Niprisan’ a kasar nan.

Adewole ya bayyana cewa gwamnati ta saka hannu a takardar yarjejeniyyar amincewa kamfanin sarrafa magunguna na ‘May and Baker’da ma’aikatar binciken magunguna na kasa (NIPRD) domin sarrafa maganin cutar.

HANYOYIN KULA DA MAI CIWON SIKILA

Kamar yadda aka sani ciwon sikila ciwo dake hana mai dauke da shi girman jikin sannan, a kullum za kaga yana rashin lafiya.

Domin guje wa irin wadannan matsaloli likitoci sun lissafa hanyoyi shida da za a kiyaye.

1. Kamata ya yi mai dauke da cutar na shan ruwa ko kuma abinci mai ruwa ruwa domin guje wa bushewar jiki.

2. Cin kayan abincin dake kara karfin garkuwan jiki na da mahimmanci ga mai dauke da cutar.

3. Yin allurar rigakafi da tanada magungunan kara karfin garkuwan jiki da wanda ke kashe ciwon jiki na da mahimmanci.

Share.

game da Author