An shiga mako na biyu kenan, tun bayan da Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta bada umarnin a yi gaggawar janye manyan motocin da suka yi dandazo a Apapa da kewaye.
An dai bada wannan umarni ne tun a ranar 22 Ga Mayu, tare cewa: “a gaggauta cire manyan tireloli da ke ajiye kan gadoji da titina cikin Apapa da kewayen Apapa.”
Yayin da PREMIUM TIMES ta kai ziyara Apapa da kewaye a ranar Asabar, ta gani da idon ta cewa wadannan tireloli da tankokin motoci na nan jibge a Apapa da kewaye kan hanyar Tsibirin Tin Can.
“Babu wani abu da ya canja tun daga unguwar Mile 2 har zuwa Tsibitin Tin-can”, haka wani ejan ya shaida wa wakilinmu, amma ya ce kada a mabaci sunan sa.
Da PREMIUM TIMES ta ziyarci Hanyar Apapa zuwa Oshodi, wani direba ya ce cinkoson motoci ya ragu. “Idan da Buhari bai bda wannan umarni ba, to da hanya ba za ta yi saukin bi ba har zuwa yanzu.”
Yayin da aka kwashe motocin da ke kan gadar Eko Bridge har zuwa cikin Ijora, su kuma na kan hanyar zuwa Ijora daga Constain na nan a cunkushe.
Motocin da aka jibge a kan titin Second Rainbow zuwa Apapa har zuwa Apapa, su na nan, ba a kwashe su ba.
“Na shafe kwanaki 12 domin kokarin na matsa da mota ta daga Sanya zuwa Mile 2” Haka wani direba mai suna Johnson ya shaida wakilinmu.
Wani direba mai suna Abiodun ya ce ya shafe kwanaki bakwai ya na kokarin dauke motar sa daga kan titin mahadar La Casera zuwa Mile 2, a tafiyar da ba ta wuce kilomita uku ba.
Johnson kuwa ya kara shaida cewa babu wani jami’inn tsaro da ya zo ya fatattake su.
Ya ce su ma ba da son ran su motocin su ke ajiye a wuraren ba.