CIN KOFIN NAHIYAR AFRIKA: Jerin wadanda zasu fara wasa tsakanin Najeriya da Guinea

0

A ci gaba da kafasawa da ake yi a Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Afrika a Masar, mai horas da ‘yan wasan Najeriya, Gernot Rohr, ya ajiye kaftin na Najeriya, Mikel Obi a kafasar da za a yi da kasar Guinea.

Dama kuma jama’a da dama sun rika kukan cewa tunda dai Obi dai tabuka abin kirki a wasan da Najeriya ta kara da Burundi ba, to kamata ya yi a wasa na gaba a ajiye shi kawai.

Sauran canje-canjen da ya yi sun hada Odion Ighalo, wanda ya ci kwallo daya a wasa da Burundi, shi ne zai fara wasa ba Paul Onuachu ba.

Haka nan kuma Moses Simon zai fara wasa ba Sanuel Chukwueze dan shekara 20 ba.

Har yanzu Shehu Abdullahi bai gama warkewa daga ciwon da ya jib a. Don haka Chidozie Awaziem ne ya ci gaba da hawa kan lambar sa a jerin masu tasron baya.

Yayin da Leon Balogun zai fara wasan sa na farko na cin Kofin Afrika, inda zai maye gurbin William Troost-Ekong.

Shi kuma Ahmed Musa zai fara bayan a wasan Burundi sai daga baya aka saka shi.

GA SUNAYEN SU NAN SU 11: Daniel Akpeyi, Kenneth Omeruo, Leon Balogun, Ola Aina, Chidozie Awaziem, Wilfred Ndidi, Oghenekaro Etebo, Alex Iwobi, Ahmed Musa, Moses Simon, da Odion Ighalo.

Share.

game da Author