CIKIN 2018: Na shafe kwanaki 124 a hannun ’yan sanda –Dino Melaye

0

Sanata Dino Melaye daga Jihar Kogi, ya bayyana a ranar Alhamis cewa a cikin 2018 ya shafe kwanaki har 124 a hannun jami’an ‘yan sanda daga arangamar su da dama da suka yi a cikin shekarar da ta gabata.

Ya ci gaba da cewa ranar da ‘yan daba suka afka cikin Majalisar Dattawa za ta kasance ranar da ta fi saura bakin ciki a shekaru hudu na zangon Majalisar Dattawa da ya shude a wannan makon.

Melaye yayi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke jawabin bankwana da Majalisar Dattawa ta shirya jiya Alhamis.

Sanatan ya fara bayani ne da jinjina wa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki saboda jajircewar sa wajen tabbatar da cewa bai zama rakumi da akala ba.

Ya kuma tunatar da cewa ya sha bayyana Saraki a matsayin Shugaban Majalisar da ba a iya tsigewa, musamman lokacin da gwamnatin tarayya ta matsa masa lamba, har ta maka shi kara a Kotun CCT.

“Ni kai na a lokacin da Gwamnan Jihar Kogi ya shirya yi min kiranye, ai ina tsare a hannun jami’an ’yan sanda. Amma ga ni a yau ina mai godiya ga Ubangiji.

“A cikin 2017 an kama ni sau takwas. Cikin 2018 an damke ni sau 18, inda na shafe kwanaki 124 daga cikin kwanaki 365 na shekara daya.

“Kwana hudu kawai na samu na yi kamfen a zaben 2019, kuma na yi nasara. Don haka ba ni da wani dalilin da ba zan nuna godiya ta ga ubangiji ba. Gwamnatin Tarayya ta maka ni kotuna daban-daban.
Amma duk da haka sai da na sake dawowa Majalisar Dattawa a matsayin Sanata.”

Daga nan kuma ya kara da cewa ba zai amince ko ya bada goyon baya Majalisa ta zama a karkashin wasu ‘yan amshin Shatan shugabannin wata jam’iyya ba.

Kafin Dino Melaye ya kammala jawabin sa, ya yi abin dariya a lokacin da ya gwasale Sanata Akpabio, wanda ya fadi zabe bayan ya koma jam’iyyar APC.

“Kai kuwa Sanata Godswill Akpabio, ina sanar da kai cewa har yanzu mu na tare da kai, domin duk da dai ba ka sake dawowa Majalisar Dattawa ba, ai za mu rika haduwa a kan titi a Abuja mu na gaisawa.”

Wannan ya sa kusan akasarin dattawan da ke cikin zauren majalisar sun bushe da dariya.

Share.

game da Author