Buhari ya nada Mele Kyari, sabon shugaban NNPC

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi sanar da nadin sa na farko tun bayan rantsar da shi shugaban kasa a Mayu.

Shugaba Buhari ya amince da nadin Mele Kyari a matsayin sabon shugaban Kamfanin mai na Kasa, NNPC.

Kakakin NNPC Ndu Ughamadu ya sanar da haka a takarda da ya fitar ranar Alhamis.

Tuni har tsohon shugaban kamfanin Maikanti Baru ya aika da sakon taya murna ga sabon shugaban.

Baya ga nadin Kyari, an nada wasu manyan darektoci 7

Ga sunayen su

1 – Roland Onoriode Ewubare (Kudu Maso Kudu) – Shugaba – Hako Danyen Mai – Chief Operating Officer, Upstream

2. Mustapha Yinusa Yakubu (Arewa Ta Tsakiya) – Shugaba – Albarkatun Mai

3. Yusuf Usman (Arewa Ta Gabas) – Shugaba – Iskar Gas da Wuta

4. Lawrencia Nwadiabuwa Ndupu (Kudu maso Gabas) Shugaba- Hannayen Jari da Kamfanoni

5. Umar Isa Ajiya (Arewa Maso Yamma) – Shugaba – Harkokin Kudi

6. Adeyemi Adetunji (Kudu Maso Yamma) – Shugaba – Harkokin Mai

7. Farouk Garba Said (Arewa Maso Yamma) – Shugaba- Ayyaukan Cikin Gida.

Share.

game da Author