Buhari ya canja sunan filin wasa na Abuja zuwa ‘ Filin Wasa na Moshood Abiola

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya canja suna filin wasa na Abuja zuwa filin wasa na Moshood Abiola.

Buhari ya bayyana haka ne a jawabin ranar dimokradiyya da yayi a Abuja.

Buhari ya kara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da samarwa mutane ababen more rayuwa sannan kuma za a maida hankali wajen samarwa mutane aikin yi da tsaro.

Ya ce an samu nasara sosai a kasa Najeriya tun bayan darewa kujeran shugabancin kasarnan.

Ya kara da cewa tabbas gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wadanda ke neman tada zaune tsaye.

Share.

game da Author