Boko Haram sun diran wa barikin Gajiram, sun kashe Sojoji 18

0

Boko Haram sun diran wa barikin sojoji dake Gajiram, dake karamar hukumar Ngazai jihar Barno sun kashe sojoji 18 sannan kuma wasu shida sun tsira da rauni.

Majiyar mu ya shaida mana cewa Boko Haram sun yi wa barikin diran bazata da misalin karfe 4 na yamma inda suka rika bude musu.

Baya ga harin sun tafi da manyan bindigogi da kayan yaki.

Sai dai kuma bayan haka rundunar Soji ta aika da dakarunta domin kai wa wannan bariki agaji.

A rahoton da muka samu zuwa yanzu, Boko haram din sun amshe wannan bariki yana hannun su.

Wannan yana daga cikin jerin sabon salon hare-haren da Boko Haram suke kai wa barikin sojoji dake Barno.

Idan ba a manta babban hafsan sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya gargadi sojojin Najeriya da su maida hankali wajen ganin sun kawo karshen Boko Haram a Kasar nan. Buratai ya ce sojojin Najeriya na neman su zama matsorata. Ya kara da cewa ba za a rika kara wa wani soja girma ba sai ya nuna bajinta.

Share.

game da Author