Gwamnatin Birtaniya ta kwace dala milyan 211,000,000, kwatankwacin naira bilyan 82 daga wani asusun ajiya na wani banki a Jersy, wanda aka hakkake cewa kudin da marigayi Sani Abacha ya boye ne.
Abacha ya yi mulki a Najeriya sama da shekaru biyar. Ya mutu a ranar 8 Ga Yuni, 1998.
Wani rahoto da wata kafar yada labarai UK Metro ta ruwaito, ta ce kudaden na boye a birnin Jersey a cikin asusun Doraville Prpperties Corporation, mallakar kamfanin wanda ke a Tsibirin Virgin Island, da ke karkashin mulkin Birtaniya.
Rahoton ya ci gaba da cewa a yanzu wadannan makudan kudade gwamnati ta kwace su, har zuwa lokacin da Jersey, Amurka da Najeriya za su amince yadda za a yi da kudaden.
“Duk wasu kudade, ko da sun kai nawa, idan aka kwace su a Jersey, za a adana su a cikin Asusun Kudaden da aka kama na Sata. Ana amfani da wadannan kudade wajen gudanar da manyan ayyuka. A baya, an yi amfani da irin wadannan kudade wajen gina ofishin ‘yan sanda da kuma fadadawa da inganta gidan kurkukun La Moye.
“Ana kuma kyautata zaton cewa za a kara kwato wasu makudan kudaden daga asusun kudin Doraville, sannan a maida su cikin Asusun Tara Kadarorin Sata a nan gaba.” Haka rahoton ya nuna.
Tun cikin 2014 aka fara tirka-tirka a kotu a kan wadannan kudade, bayan da mahukuntan Amurka suka nemi Antoni Janar na tsibirin da ya sa kotun Royal Court ta haramta wa Doraville kudaden.
Yayin da kamfanin Doraville shi kuma ya shigar da ba’asi a kotu inda ya nemi a kori karar da aka shigar a kan kudaden da aka samu cikin asusun ajiyar sa.
Sai dai kuma kutu ta yi watsi da bukatar kamfanin a cikin 2016. Cikin 2017 kuma Doraville ya daukaka kara, a Kotun Daukaka Kara, amma bai yi nasara ba.
Idan ba a manta ba, Shugaba Buhari ya sha nanata cewa marigayi Sani Abacha bai saci ko kwabo daga dukiyar Najeriya ba. Sai daga baya aka rika maido wasu makudan kudade da aka ce ya wawura ya kimshe a kasashen waje.