BINCIKE: Mutane sama da miliyan daya ne ke kamuwa da cututtuka irin na sanyi duk rana a duniya – WHO

0

Sakamaon binciken da Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa mutane sama da miliyan daya ne ke kamuwa da cututtuka na sanyi a rana a duniya.

A shekara kuwa adadin yawan mutanen dake kamuwa da irin wadannan cututtuka sun kai miliyan 376.

Sakamakon binciken ya kara nuna cewa cututtukan sanyin da aka fi kamuwa da su sun hada da ‘Chlamydia, Gonorrhoea, Trichomoniasis da Syphilis sannan mutane masu shekaru 15 zuwa 49 ne suka fi kamuwa da cututtukan.

Jami’in WHO Peter Salama ya ce akan kamu da wadannan cututtuka ta hanyar amfani da bandaki wadda bashi da tsafta, karin jini da sauran su amma binciken ya nuna cewa mutane sun fi kamuwa da cutar a ta hanyar jima’i.

Salama ya ce cututtuka irin haka na yaduwa ne a dalilin rashin shan maganin kara karfin garkuwan jiki wato ‘Antibiotics’ da rashin sani.

“ A bisa wannan sakamako muke kira da cewa lokaci yayi da ya kamata a zo a hada hannu domin dakile ci gaba da yaduwar wwadannan cutuka.

“Dakile yaduwar wadannan cututtuka ya zama dole ganin cewa cututtuka irin haka na hadasa rashin haihuwa a maza da mata, samun barin ciki, kisan jarirai, kamuwa da cututtukan dake kama zuciya, kamuwa da cutar kanjamau da sauran su.

“Idan ba a manta ba a 2016 duniya ta rasa jarirai 200,000 a dalilin kamuwa da cutar Syphils sannan mutane da dama sun kamu da matsalolin da ya shafi kiwon lafiyar su a dalilin wannan cutar’’.

Salama ya ce domin samun mafita kamata ya yi gwamnatocin duniya da ma’aikatan kiwon lafiya su hada hannu wajen wayar da kan mutane kan hanyoyin guje wa kamuwa da wadannan cututtuka.

HANYOYIN GUJEWA KAMUWA DA CUTUTTUKAN

1. Yin gwajin wadannan cututtukan lokaci lokaci musamman ga mata masu ciki.

2. Yin amfani da kwaroro roba a duk lokacin da za a sadu.

3. Tsaftsace bandaki.

4. A rika shan magungunan kara karfin garkuwar jiki wato ‘Antibiotics’ yadda likita ya umurta domin gujewa matsalar rashin aikin magani a jikin mutum.

5. Kauracewa jima’i kokuma samun mutum daya wanda za a rika saduwa da shi

6. Gujewa kamuwa da cututtuka kamar su kanjamau, hepatitis da sauran su.

Share.

game da Author