BINCIKE: Kashi 75 bisa 100 na matan Najeriya na shafe-shafen man canja kalan fata

0

Wasu kwararru a fannin hada man dake canja launin fata sun bayyana cewa lallai yin amfani da ire-iren wadannan mai na da matukar hadari ga lafiyar mutum.

Sun ce yanzu mata da masu yin haka sun fi yin amafani da Allura ne da ke kunshe da ‘Glutathione’.

Duk da cewa Masanan sun akan samu kwayar‘Glutathione’ a cikin jikin mutum kuma yana taimakawa wajen kara karfin garkuwan jiki da hana mutum kamuwa da cututtuka.

Baya ga haka shi wannan sinadari da canja launin fatar mutum da kuma kawar da tabo idan yana da shi.

Shi dai kokarin canja launin fata bai tsaya ga mata ba kawai a wannan zamani domin har maza ma suna yin haka.

Wata mata da ta kware a hada man ire-iren wadannan mai dake kasuwar Wuse a Abuja tace ta dade a wannan harka.

Mrs Haruna ta ce duk da cewa mutane sunfi yin amfani da kwayoyi da yin alluran ‘Glutathione’har yanzu wasu na amfani da na mai ne cewa babban dalili kuwa shine don irin tsadan da kwayoyi da allura ke da shi.

Tace ita nata man nada arha matuka.

Sai dai kuma a inda gizo ke sakan shine Ma’aikatar Kiwon lafiya ta sanar cewa yin amfani da irin wadannan mai da su Mrs Haruna ke hadawa, wato ‘Organic Cream na da hadarin gaske sannan yana kawo cutuka kamar su daji, cutar koda, hawan jinni da dai sauran su.

Duk da irin wadannan hujjoji matsauri da ban tsoro da ake ta yi wa mutane gargadi da bai hana su cigaba da amfani da ire-iren wadannan mai ba.

Ra’ayoyin Mutane

Wata matashiya mai suna Rita Ameh ta bayyana wa wakiliyar mu cewa ta fara amfani da man canja kalan fata ne saboda maza sun fi son jajajen mata, wato masu haske.

“Tun da na gano hakane riba na dukufa wajen amfani da wadannan kayan shafe-shafe domin kara kyau da farin jini ga maza.

Shi kuwa Uche Clement mai siyar da jakukkuna a kasuwar Wuse gazgata maganar Rita yayi yana mai cewa tsakani da Allah a yanzu kam maza sun fi yin mu’amula da jajayen mata fiye da bakar mace.

Sakamakon Bincike

Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashen Nahiyar Afrika da aka fi yawan amfani da mai da magungunan dake canja launin fata.

Sakamakon binciken ya nuna cewa kashi 77 bisa 100 na matan Najeriya na amfani da kayan shafe-shafen da ke canja kalan fatan mutum, daga Najeriya sai kasar Togo dake da kashi 59 bisa 100 sannan kasar Afrika ta kudu dame da kashi 35 bisa 100 da Mali dake da akalla mata kashi 25 bisa 100 da ke muamula da kayan shafe-shafen dake canja launin fatar mutum.sannan a kasar Mali mata kashi 25.

A dalilin bayanan rahotonnin da ake ta samu na sakamakon bincike da kwararru suka yi akan wannan abu, dole sai gwamnatin kasashen Afrika sun mike tsaye wajen yi wa shigowa, sarrafawa da amfani da kayan shafe-shafen da mutanen kasashen su ke amfani da.

Share.

game da Author