Bayan ganawa da suka rika yi a tsakanin su tun ranar Asabar zuwa safiyar yau Talata, gwamnonin APC tare da shugaban su Adams Oshiomhole sun yi wa majalisar kasa diran mikiya.
Idan ba a manta ba a yau Talata ne za a yi zaben shugabannin majalisar Dokoki ta kasa.
Sai dai kuma ba a nan bane gizo ke sakar domin kuwa dan takaran da APC suke yi wa yakin zama shugaban majalisun duk cikin su ya duri ruwa ganin cewa babu wanda ya san yadda za ta kaya.
Ali Ndume wanda shine dan bowa ya rantse ba zai janye wa zabin shugaban kasa da APC ba cewa shima yana da ‘yancin a fafata dashi.
Su ko PDP cewa suka yi tabbas ba za su zabi abin APC ba, Ali Ndume zasu zaba sannan sunyi kira ga mambobin su da su zabi Ndume din.
Yanzu dai kowa ya hallara, shi kansa Akawun majalisar ya iso majalisar.
YANZU – 11:20
KAI TSAYE DAGA MAJALISA: Sanatoci sun tada kowa cewa da magatakardan majalisa yayi wai fa za a yi zabe ne a asirce daga kai sai kuri’ar ka ba a bayyana ne, wato kowa ya gani.
Amma yanzu dai an amince za a rika kira ne mutum na zuwa ya jefa kuri’ar sa. Tuni ma har an fara kada kuri’a
ZABEN MAJALISA: Ahmad Lawan ya doke Ali Ndume
Lawan ya samu kuri’u 76, shi kuma Ndume ya samu kuri’u 28