Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana wa Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa cewa ba ta mallaki wani runbun tattara bayanan sakamakon zabe da a Turance ake kira ‘server’ ba.
INEC ta yi wannan bayani jiya Alhamis a kotun a Abuja.
Wannan bayani ya biyo bayan karar kalubalantar zaben shugaban kasa da PDP tare a dan takarar ta Atiku Abubakar suka shigar da APC, Shugaba Muhammadu Buhari da kuma INEC kan ta.
A cikin karar da Atiku ya shigar, ya yi ikirarin cewa sakamakon da INEC ta bayyana daban, wanda ke cikin rumbun tattara sakamakon zaben ta kuma, wato ‘server’ daban.
Atiku ya yi ikirarin cewa shi ne ya yi nasara a kan Buhari da ratar kuri’u masu yawa, kamar yadda ya ce ita ‘server’ din ta nuna.
Daga nan PDP da Atiku sun nemi kotu ta ba su damar duba wannan rumbun ajiyar kididdigar alkaluman zabe, wato ‘server’ da suka yi ikirarin INEC ta mallaka.
Sai dai kuma lauyan INEC mai suna Yunus Usman, ya roki kotu ta yi watsi da wannan zargi, domin har ma gara tatsuniya da shi. Ya ce INEC ba ta da wata ‘server’ da ta tattara sakamakon zabe, kamar yadda PDP da Atiku suka yi zargi.
Ba za mu bada abinda bamu da shi ba
Lauyan INEC Usman ya ci gaba da cewa abin akwai daure kai, domin Atiku da PDP na son INEC ta ba su abin da ba ta da shi, kuma abin da ba ta taba yi ba, ballantana har a ce INEC ta mallake shi.
“Su fa so suke yi mu ba su abin da mu kuma ba mu da shi.” Inji Usman.
Daga nan kuma ya jawo hankalin kotu a kan hukuncin da ta yanke ranar 6 Ga Maris, inda ta bai wa PDP damar duba kayan da aka gudanar da zaben 2019, wanda babu maganar rumbun tattara sakamako, wato ‘server’ a ciki a lokacin.
Dukkan lauyoyin Shugaba Buhari, wato Wole Olanipekun da kuma na APC, wato Lateef Fagnemi sun nemi a kori rokon da PDP da Atiku suka yi.
Zargin da PDP da Atiku suka yi ya nuna a cewar su sun samu bayanan sakamakon zaben da suke ikirari ne a cikin wannan rumbun ajiya mai lamba: “INEC_PRES_RSLT_SRV2019, kuma mai adireshin Mac 94-57-A5-DC-64-B9 wanda ke da lambar Microsoft ID 00252-7000000000-AA535.” Inji su Atiku.
Discussion about this post