Jam’iyyar APC mai mulki ta tsaida Sanata Ovie Omo-Agege a matsayin wanda ta ke so a zaba Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Omo-Agege Sanata ne da ke wakiltar Shiyyar Jihar Delta ta Tsakiya.
Sannan kuma ta bayyana cewa Hon. Idris Wase daga Jihar Nassarawa a Matsayin Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.
Yayin da Omo-Agege zai fito a matsayin mataimakin Sanata Ahmed Lawan, shi kuma Wase zai fito a matsayin mataimakin Femi Gbajabiamila.
Sanarwar wannan matsaya da APC ta cimma ta fito ne daga Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na Kasa, Lanre Issa-Onilu.
Ya ce Kwamitin Zartaswar APC na Kasa ne ya cimma wannan matsaya bayan taron da suka gudanar a ranar Asabar da Lahadi da ta gabata, wato 8 da kuma 9 Ga Yuni, 2019.
Onilu ya kara bada hasken cewa an cimma wannan matsaya bayan an tuntubi Shugaba Muhammadu Buhari kuma ya amince.
Wannan sanarwa ta na nufin Omo-Agege zai yi takara ne tare da Sanata Ahmed Lawan a matsayin mataimakin sa, domin shi Lawan din APC ta tsaida takarar Shugaban Majalisar Dattawa.
Omo-Agege shi ne gogarman da ya ja zugar wasu kartin matasa ’yan takife, suka kutsa Zauren Majlisar Dattawa, har suka sace Sandar Mulkin Majalisa.
Duk da cewa dai ya musanta wannan zargi, amma dai kwamitin bincike da Majalisar Dattawa ta kafa, ta same shi dumu-dumu da aikata wannan laifi.
Har ila yau, wani binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta gudanar a lokacin, ya tabbatar da cewa Omo-Agege dai ya dauko sojojin hayar wadannan matasa ’yan Arufta, wadanda suka kutsa cikin majalisar har suka sace Sandar Mulki.
Duk da cewa an gano sandar mulkin daga baya, har yau babu ko mutum daya da aka gurfanar kotu ko aka hukunta dangane da wannan sata.
Discussion about this post