Hadaddiyar kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya na jihar Barno (MHWUN) ta yi kira ga gwamnati kan karo mata ma’aikata 4,000 domin inganta fannin kiwon lafiyar jihar.
Kungiyar ta yi wannan kira ne ganin yadda rashin isassun ma’aikatan ke ci wa samar da kiwon lafiya a jihar tuwo a kwarya a asibitocin jihar.
Shugaban kungiyar Yusuf Inuwa ya ce fannin kiwon lafiyar jihar zai bunkasa ne idan gwamnati ta dauki sabbin ma’aikata a asibitocin jihar.
A kwanakin baya ne wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya suka koka a
kan yawan mutuwan yara da mata da ake samu a kasar nan.
Ma’aikatan kiwon lafiya ta fadi haka ne bayan rahotan yawan mutuwan yara da mata da kungiyar WHO, Asusun UNFPA da Asusun UNICEF suka bada a taron wayar da kan mutane kan illolin rashin samun ingantaccen kiwon lafiya da ya gudana a kwalejin koyar da aikin likitanci dake jihar Legas.
A jawabin ta babban bakuwa Olusola Odujinrin ta ce har yanzu akwai sauran rina a kaba domin dole sai Najeriya ta kara maida hankali wajen inganta fannin kiwon lafiyar kasar, ba za a kai ga ci ba.
Bayan haka Odujinrin ta ce daya daga cikin matsalolin da ke gurgunta fannin kiwon lafiya musamman cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko shine karancin kudi.
” Har yanzu ana matukar fama da rashin kudi a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, babu likitoci sannan babu kayan aiki.