An yi garkuwa da matar shugaban kungiyar kwadago na jihar Taraba

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da uwargidan shugaban kungiyar kwadago na jihar Peter Gambo, Abigail Gambo da wani makwabcinsa dake da mallakin kamfanin buredi mai suna ‘Our Nation Bread’ Emeka Okoronkwo.

Kakakin rundunar David Misal ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranan Alhamis a garin Jalingo.

Misal yace masu garkuwa da mutanen sun sace Abigail da Emeka a gidajen su dake Magami da karfe daya na Asuban Alhamis.

” Maharan sun harbi wani mutum a kafa a lokacin da suke kokarin sace wadannan mutane biyu a Magami.

Shugaban kungiyar kwadagon Gambo ya tabbatar da haka inda ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun far wa gidan sa da safiyar Alhamis ne suna harbi ratatata babu birki.

Ya ce sun tafi da matarsa zuwa wani wurin da bai sani ba sannan har yanzu basu tuntubeshi game da biyan kudin fansar matar sa ba.

A yanzu haka likitoci na duba mai gadin gidan Emeka makwabcin Gambo da aka harba a kafa a asibiti.

Share.

game da Author