An yi garkuwa da Dagacin garin Labo, jihar Katsina

0

Mahara sun arce da Dagacin garin Labo, dake karamar hukumar Batsari, a jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Katsina Gambo Isa ya bayyana cewa a ranar Talata ne mahara suka far wa kauyen Labo suna ta harbe harbe daga nan sai suka far wa gidan dagacin sannan suka tafi tashi.

Gambo ya ce bayan an sanar da su wannan hari sai suka fantsama kauyen domin farautar wadannan ‘yan ta’adda.

Yanzu dai muna nan muna bin diddigin wannan aika-aika sannan kuma muna rokon mutane da su hakura da zuwa gonakin su dake kusa da dajin Rugu.

Sannan kuma rundunar ‘yan sandan na kira ga mutane da su rika kai rahoton ayyukan mutanen da basu amince da su ba da kuma taimakawa ‘yan sanda da bayan sirri.

Share.

game da Author