An kashe akalla mutane 25,794 a hare-hare daban-daban a fadin kasar nan, daga ranar da aka rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari, wato 29 Ga Mayu, 2015, zuwa 29 Ga Mayu, 2019.
Wani rahoto ne wanda PREMIUM TIMES ta bi diddigin bayanan da ya yi, kuma ta babbatar da haka.
Kididdigaggun alkaluman matattu da ke hannun Kungiyar Bin Diddigin Bayanan Tsaro, wato Nigeria Security Tracker (NST) ya nuna cewa “wadannan hare-hare na da nasaba da siyasa, matsin tattalin arziki da kuma takaici da kuncin zamantakewar yanayin da al’umma ke ciki.”
Wannan kungiya da ta bada himma wajen tattara bayanan matsalolin tsaro a Najeriya, ta ce duk ta tattara bayanan ta ne ta hanyar amfani kafafen yada labarai na cikin gida Najeriya da na kasashen waje.
Wannan rahoto ya nuna cewa matsalar tsaro a Najeriya ta fara kamari da tun daga 29 Ga Mayu, 2011, bayan rantsar da shugaba Goodluck Jonathan.
Rahoton ya ci gaba da cewa rantsar da Jonathan “ya kara haifar da ruruwar darewar hadin kan kasa zuwa bangaranci, shiyyanci da kuma batutuwa na addinanci.”
“Boko Haram sun rika cin karen su babu babbaka a Arewacin Najeriya. An kuma rika samun tashe-tashen hankulan fadace-fadacen kabilanci, manoma, makiyaya har wani lokacin rikice-rikicen kan rikide su koma na addini.
“An samu bayyanar wasu ’yan takife daga yankin Neja Delta mai arzikin danyen man fetur. Sannan kuma sojoji sun rika kashe fararen hula bagatatan. ’Yan sanda kuwa sun yi kaurin suna wajen kashe jama’a ba tare da an yanke musu hukunci a kotuna ba.
A cikin watan Yuli, 2015, an kashe mutane 1,299 sai kuma cikin Janairu, 2019 aka kashe mutane 1,077.
Rahoton ya ci gaba da nuna cewa Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 5,598, yayin da makiyaya da mahara suka kashe sama da 4,000.
Su kuma sojoji da ’yan sanda sun kashe mutane 4,068.
Sai dai kuma duk da wannan kisan rubdugu da kisan-kiyashi, Shugaba Muhammadu Buhari na ta nanata cewa an kawar da matsalar tsaro, kuma an murkushe Boko Haram.
Cikin Fabrairu, tsohon Ministan Yada Labarai Lai Mohammed yace a yanzu an gama da Boko Haram, amma Najeriya Na fuskantar fada ne da iyayen gidan Boko Haram, wadanda suka addabi duniya, wato ISWAP.
Ya ce wannan kasaitacciyar kungiya mai shuka ta’addanci a doron duniya, yanzu sun ginu kuma sun kafu a Afrika ta Yamma.
Discussion about this post