An kama masu garkuwa da mutane 10 a jihar Kebbi – ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta bayyana cewa ta yi nasarar kama bata gari 32, masu garkuwa da mutane 10 sannan da wasu dake hada baki da masu garkuwa da mutane su uku.

Kwamishinan ‘yan sanda Garba Danjuma ya sanar da haka wa manema labarai a makon da ya gabata.

Danjuma ya ce rundunar ‘Operation Puff Adder’ ce ta kama wadannan mutane a tsakanin watannin Mayu da Yuni.

“Mun kama su dauke da bindigogi, wayoyin Komfutoci, igiyoyin wutan lantarki, wukake da adduna.

“An fara kama masu hada baki da masu garkuwa da mutanen ne su uku a karamar hukumar Danko\Wasagu.

“Sauran bata garin da muka kama sun aikata laifukan da suka hada da fashi da makami,satan babura,fyade da yawo da makamai a jikin su.

Danjuma yace da zarar an kammala gudanar da bincike akan su za a gabatar da su kotu.

Share.

game da Author