Likitoci sun bayyana cewa yin amfani da dabarun bada tazarar iyali baya sa a kamu da cutar kanjamau.
Wannan ya biyo bayan rade-radin da ake ta yadawa cewa wai yin amfani da dabarun bada tazarar iyali na iya sa a kamu da Kanjamau.
Kasashen Eswatini, Kenya, Afrika ta Kudu Zambia na daga cikin kasashen duniya da suka fi yawan mutanen dake dauke da kanjamau da kuma kasashen da suka fi yin amfani da dabarun tazarar iyali.
Mutane na ganin cewa dabarun ba da tazarar iyali da suka hada da allura, yin ashanar hannu da wanda ake sakawa a mahaifar mace na sa a kamu da kanjamau.
Likitoci sun bayyana cewa mutum zai iya kamuwa da kanjamau ta hanyar jima’I, karin jini,amfani reza ko allurar wanda ke dauke da kwayoyin cutar da sauran su amma ba ta hanyar amfani da dabarun bada tazarar iyali ba.
Akan sami matsala da dabaran bada tazaran haihuwa ne idan dabaran da mace ke amfani da shi bai dace da jikinta amma babu abinda hada shi da yin amfani da wani tsari na bada tazar iyali.
A wani bincike da akayi a shekarar 2015 akan ba da tazarar iyali ya nuna cewa mafi yawa-yawan matan da ke amfani da dabarun ba da tazara iyali ya karu matuka a Najeriya.
A binciken da hukumar Kididdiga wato ‘National Bureau of Statistics’ ta yi ya nuna cewa a shekaran 2014 kashi 23 bisa 100 na mata ne ke amfani da dabarun amma a shekarar 2015 ya karu inda ya kai kashi 30 bisa 100.
PREMIUM TIMES ta tattauna da wadansu magidanta da Mata kan yadda suke amfani da dabarun kayyade iyali.
Wata mazauniyar garin Abuja Aisha Jamiu ta ce hakika tasan mene ne ake nufi da dabarun ba da tazarar haihuwa kuma tana amfani dashi matuka.
Ita kuma Janet Asumu ma’aikaciyar gwamnati ta ce lallai ta tsorata da maganganun bisa ga irin maganganun da mata ke fadi game da shan maganin.
Ta ce ta fi yin amfani da dabarun gargajiya kamar kirga kwanakin ganin al’ada, amfani da wasu sauyoyin itatuwa, zubar da maniyi a waje da maza kan yi a lokacin saduwa da dai sauran su.
Janet Asumu ta ce amma bayan anyi mata bayani sosai ta amshi tsarin.