Maganar Almajirci ya dade ana tattauna batun yadda za a kawo karshen shi a yankin Arewacin Najeriya.
Mutane da dama na ganin babban matsalar da ya fi zama abin da gwamnatocin Arewa zasu maida hankali akai shine ganin yadda za a kawo karshen wannan mummunar hanya na koyar da yaran mu addini.
Maimakon a koyar da yara karatu, tura yara karatun Allo yanzu ya zama sana’a da ake cin riba da shi sosai.
Malaman dake amfani da irin wadannan yara kanyo jigilarsu ne daga kauyuka da sunan wai za a kawo su su koyi karatun addini.
Iyayen su kuma su nado kayansu su mika su, babu ruwansu da cin dan ko shansa.
A kwana a tashi yaro sai kaga ya gagari malaminsa ya fada sana’ar banza, ko shaye-shaye ko sata.
A lokacin da suke tare da malaman na su banda yawon bara a kwararo-kwararo, lungu-lungu, gida-gida, sako-sako da kuma idan yaga rabaraba ya waske da abinda ya kyalla ido ya gani maishi kuma baya kusa.
Zaka kaga yaro baiyi wanka ba sannan bai yi aski ba kullum a kalrkashin kwata ko bola yana tsince tsince.
Wannan salon karatu ya zama saidai Allah ya kyauta domin ba karatun kawai ake yi ba harda abinda yafi karatu zaka ga yaro ya fada ciki.
Yanzu akwai makarantu na islamiyya, wanda danka zai je makaranta ya dawo gabanka, amma da yake abin ba saboda Allah ake yin sa ba har yanzu wasu sun kafe cewa lallai sai an rika kawo musu yara suna karantarwa .
Yara da dama sun bace, wasu sun mutu wasu sun fada hannun matsafa wasu kuma sun kauce, maimakon rewa karatu daga karshe rera waka suka koyo a makarantun da aka tura su.
Sau da yawa zaka ga wadanda suka wahala da karatu ta hanyar Almajirci ba su kaunar ‘ya’yansu su bi wannan hanya.
Wasu da na zanta da su duk sun fadi min cewa wannan salo na karatun allo da za atura da wani gari, ba abinci, babu wajen kwana mai kyau sai aikin yi wa malami bauta da barace-barace ya zama tsohon yayi.
” Allah ya kawo mana sauki yanzu menene ya sa muke ba kan mu wahala a rayuwa tsakani da Allah. Kai da kanka ka daba wa kan ka wuka. Zamanin nan ba zamanin nesa da da bane.” Inji wani matashi da da Almajiri ne.
Matakin da gwamnati ta Dauka
Wannan mataki da gwamnati ta dauka cewa yanzu dole ne yaro ya tafi makaranta a lokacin da kowani yaro ke tafiya makaranta zai yi matukar tasiri a musamman Arewa.
Dole sai Buhari ya toshe kunnuwar sa ya aikata abin da ya dace idan yana so ya kawo wa ya kin Arewa ci gaban da take bukata.
Dole sai Buhari ya toshe kunnuwar sa ya nuna bajintarsa a matsayinsa na tsohon soja mai kishin Arewa idan har ana so a kawo karshen wannan bakin hanyar karantar da yaran mu, wato Almajirci a Arewa.
Aikin farad daya za ayi wa wannan doka, kowa ya karantar da dan sa a garinsu. Idan kuma har zai tura dan karatu a wani garin to a tabbata makarantar kwanace, da dakunan kwana da shirin yadda za a ciyar da yaro.
Lokaci yayi da mutanen Arewa zasu hada hannu a zauna wuri daya a mara wa gwamnati baya domin ganin an kauda salon karatu na Almajircin a yankin Arewa baki daya.
Discussion about this post