Alkalin Kotun Shari’a ta 1 da ke Magajin Gari, Kaduna, ya bada umarnin a aske kan wani da ake tuhuma da aka gurfanar a gaban sa.
Wanda ake tuhumar mai suna Usman Abubakar, an gurfanar da shi kotun ne saboda zargin yayi wa wani magidanci dukan tsiya.
Mai Shari’a Lawal Dahiru, ya nuna bacin rai ganin yadda Usman ya bayyana a kotun sa da suma dugujaja a kan sa.
Ya ce kotu ba ta lamuntar shigar rashin mutunci a bayyana a gaban ta.
Daga nan sai ya umarci nan take a kira wanzami ya yi masa kwal-kwabo, domin ya zama darasi a gare shi da kuma wasu a nan gaba.
Ana tuhumar Usman dan shekara 19 da laifin lakada wa Yusuf mai shekaru 35 dukan tsiya a Rigasa, Layin Dadawa cikin Kaduna.
Yusuf ya shaida wa kotu cewa a ranar 11 Ga Mayu, wajen karfe 9 na safe, ya shiga cikin gidan su da mota, sai ya ji Usman ya na surfa masa zagi.
Ya ce a lokacin da ya tunkari Usman domin ya ji dalilin zagin sa da ya keyi, sai ya hau shi da duka ba tare da wata-wata ba.
Ya ci gaba da cewa: “Na daure, na hukura, ba tare da na rama duka na ba.
Daga nan sai na kai rahoto ofishin ‘yan sanda, inda aka kashe maganar. Aka ce ya ba ni hakuri, kuma na yarda.
“Amma bayan kwanaki kadan kuma sai mata ta ta shaida min cewa mahaifiyar Usman mai suna Hajiya Sa’adatu Shehu, ta je har gida ta rika surfa mata zagi ta na muzanta ta da sunaye munana, marasa dadin ji.
“Mahaifiyar Usman ta shaida wa mata ta wai ina kokarin kashe mata dan ta, Usman.”
Sai dai kuma Usman ya musanta zargin tuhumar dukan Yusuf da aka yi masa.
Ya ce ya na tare da abokan sa a lokacin da ya Yusuf ya dawo, ya dallara musu hasken fitilar motar sa, ya kashe musu idanu. “Maimakon ya ba mu hakuri, sai ya rika zagin mu. Amma dai ni ban doke shi ba.”
Mai Shari’a ya umarce su da su koma gida su ci gaba da zama lafiya da junan su.
Ya kuma gargade su cewa idan aka kara kawo su a gaban sa a kan wannan rigima, to za su yaba wa aya zakin ta.