Majalisar Dinkin Duniya ta yi amfani da albashin fitaccen dan kwallon nan Leonel Messi, wajen shigar da korafin yadda ake samun wawakekiyar rata tsakanin albashin ‘yan wasa maza da mata a wasanni daban-daban na duniya.
An gabatar da kakkausan korafin cewa ana nuna wa ‘yan wasa mata na duniya bambancin jinsi wajen biyan albashi, alawus da sauran hakkokin da ake amfani da su wajen daukar nauyin tallace-tallace, a matsayin su na mata fitattun ‘yan wasa.
Messi a binciken da aka gudanar, ya na samun dalar Amurka milyan 84 a duk shekara kama daga albashi, alawus-alawus da sauran kudade na daukar nauyin tallace tallace da ya ke yi wa kamfanoni masu zaman kan su.
Sannan kuma Kididdgigar da Matan Majalisar Dinkin Duniya suka yi, ta nuna cewa gaba dayan albashi da alawus-alawus na fitattun ‘yan kwallo mata su 1,693 masu buga wasannin firimiya a manyan kasashe bakwai, bai wace dala milyan 42.6 ba.
Sun rika bi a shafin sun a Facebook da sauran kafofin sadarwa na soshiyal midiya su na yayata wannan rashin adalci da bambancin jinsi da suka ce ana yi wa mata a bangarorin wasanni daban-daban a duniya.
Goal.com da sauran manyan jaridun Turai duk sun buga wannan labari.
“Mu na kiran mata su rika fitowa a filin wasannin Cin Kofin Duniya na mata da a yanzu haka ke gudana a kasar Faransa, su na yekuwar nuna rashin yadda da wannan fifikon da kuma neman a daidaita albashinmu da na maza.”
Haka suka buga a shafin na su na Facebook, kamar kuma yadda Goal.com da sauran jaridu suka ruwaito.
Tuni dai dama ‘yan wasan da ke wakiltar kasar Amurka su 28 suka maka Hukumar Kwallon Kafar kasar kotu, suka nuna cewa sun gaji da bambancin da ake nuna masu. Suka kuma nemi a daidaita albashin su da na maza.
Sai dai kuma hukumar kwallon kafar ta Amurka ta nemi a sasanta a wajen kotu, ba a gaban mai shari’a ba.