Akwai yara miliyan takwas da ke gararamba a jihohi 10 har da Abuja –UNICEF

0

Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEFF), ta bayyana cewa akwai kananan yara milyan takwas da ke gararamba kan titi ba su zuwa makaranta a jihohi 10 da Abuja a kasar nan.

Jihohin da UNICEF ta bayyana sun hada Bauchi, Neja, Kano, Katsina Sokoto, Zamfara, Kebbi, Gombe, Adamawa da kuma Taraba.

A cikin wani bayani da UNICEFF ta fitar jiya Lahadi domin tunawa da Ranar Kananan Yara na Afrika, wakilin ta na Najeriya, Peter Kawkins ya ce wasu matasa 2000 sun kai kukan korafe-korafen masu rike da mulki a wadannan jihohi cewa akwai bukatar a samar wa yara ingantaccen ilmi, musamman ma yara mata.

Kawakins ya ce rajin samar da ingantaccen ilmi a Najeriya zai matsa wa sabbin shugabannin da aka rantsar lamba tare da dora musu alhakin tabbatar da cewa sun cika alkawurran da suka dauka na samar wa kowane yaro ilmi mai inganci a Najeriya.

“Akwai yara kimanin milyan takwas da ba su zuwa makaranta sai gararamba suke yi a cikin jihohin Bauchi, Neja, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, Kebbi, Gombe, Adamawa, Taraba da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya, FCT.”

Kawkins ya kuma ce a Yankin Arewa maso Gabas akwai yara milyan 10.5 da ba su samun damar zuwa makaranta saboda rikicin Boko Haram da ake fama a yankunan su.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga rahoton wani bincike da kungiyar DHS a karkashin UNICEFF ta yi cikin 2015, cewa akwai yara milyan 13.2 da ba su samun damar karatu a Najeriya.

Rahoton ya ce gaba da cewa a Najeriya ne duk duniya aka fi samun yawaitar yaran da ba su zuwa makaranta.

Rahoton UNECEFF ya ce kashi 69 bisa 100 na yaran da ba su zuwa makaranta duk a Arewa su ke.

Share.

game da Author