Abubuwa 11 da Majalisar Tarayya za ta yi don samun goyon bayan ‘Yan Najeriya

0

A yanzu dai jam’iyyar APC za ta iya bugun kirjin cewa ita ke rike da Majalisar Tarayya da kuma Majalisar Dattawa baki daya.

Ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya rika kukan cewa Majalisar da ta sauka kwanan nan, a karkashin Bukola Saraki da Yakubu Dogara ne suka rika zame masa karfen kafa wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka a kasar nan, to yanzu dai wannan kuka ya kau.

A kan haka, wannan majalisa a yanzu ba ta da wani uziri sai fa kawai ta mike tsaye domin ta samu goyon bayan al’ummar kasar nan.

Ga wasu lakanoni nan guda 11 da majalisar za ta sha kuma ta yi wanka domin samun farin jinin al’ummar kasar nan.

1: Su bayyana wa duniya kasafin kudin da suke samu kama daga albashi da kuma alawus-alawus din su. Saboda shekara da shekaru ana zargin su da kwasar albashi da alawus fiye ma da ’yan majalisaun manyan kasashen Turai da Amurka. Sannan kuma ana korafin cewa kudaden da ake ware wa majalisa sun yi yawa, musamman ganin halin kuncin da al’ummar kasar nan ke ciki.

Ma’aikatan Majalisar Tarayya ba su kai 10,000 ba, amma kuma kasafin kudin da ake ware wa majalisa a shekara ya kai adadin kudaden da ake bai wa wasu jihohi 21 a shekara.

2: SU SOKE ALAWUS DIN DA BA YA BISA KA’IDA

Wata hanyar da ake ganin cewa majalisa za ta bi domin samun farin jinin jama’a ita ce, ta soke dukkan wasu alawus-alawus da suke karba wanda ba a bisa ka’ida ya ke ba. Kama daga kudin sayen gado da katifu da kayan alatun daki da sauran wasu alawus da suke karba a duk wata, wanda ba a cikin dokoki suke ba.

Akwai wasu kudi naira milyan 13.5 da ake bai wa kowanen su a duk wata, wadanda har wata rana Sanata Shehu Sani ya ce kamata ya yi a daina bayar da su, saboda babu wanda ya san kudin don me ake bayar da su.

3: SU DAINA JINKIRIN SAKIN KASAFIN KUDI

Wannan ma wani lakani ne wanda idan majalisa ta sha shi kuma ta yi wanka da shi, to za ta samu farin jinin al’ummar kasar nan da gaggawa.

Tun daga 2016 har zuwa 2019, Shugaba Muhammadu Buhari na kai wa Majalisa kasafinn kudi cikin Disamba, amma ba a maida masa kasafin sai cikin watan Maris. Wannan ya na nuna yadda ake daukar tsawon lokaci kasafin kudi na hannun Majalisa.

4: SU KAWO KARSHEN CUSHEN KUDADE CIKIN KASAFIN KUDI

Shekaru da dama ana zargin Majalisa na cushen makudan bilyoyin kudade a cikin kasafin kudi da sunan gudanar da wasu ayyuka. An kuma tabbatar da cewa wasu kudaden duk a cikin aljifan su suke sulalewa.

Cikin kasafin 2018 sun yi cushen ayyuka na naira biliyan 578, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya zarge su da yi.

Ko a cikin na 2019 sai da Buhari ya yi korafin cewa sun cusa naira bilyan 90 a ciki.

Don haka a wannan zangon ‘yan Najeriya na fatan Sanata Ahmed Lawan zai kawo karshen wannan kumbiya-kumbiya.

5: SU SOKE KUDADEN AYYUKAN MAZABU

A kowace shekara akwai naira bilyan 100 da Majalisar Tarayya da ta Dattawa ke warewa domin a ba su ayyukan da za su yi wa mazabun su. Daga cikin kudin, Majalisar Tarayya mai wakilai da yawa na karbar kashi 60 bisa 100, ita kuma Majalisar Dattawa na karbar kashi 40 bisa 100.

Rahotanni da dama na nuna cewa akasari ana karkatar da wadannan kudaden ne kawai.

5: SU DAINA KARBAR KUDADEN SAYEN BARGAR MOTOCI

Daya daga cikin manyan dabi’un ‘yan majalisar da suka gabata, ita ce dabi’ar sayen bargar motoci. Sannan da yawa daga cikin su duk sun dawo majalisa, da su za a sake cin wannan zango na 2019 zuwa 2023.

Wasu takardun bayanai da suka fado a kan teburin PREMIUM TIMES sun tabbatar da cewa a 2018 an ware naira biyan 6.6 domin sayen tamfatsa-tamfatsan motocin ‘Yan Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya.

Bayanai sun kara tabbatar da cewa ‘yan kwangila 27 ne suka yi aikin jigilar wadannan motocin.

Ko a cikin 205 ma sai da aka ware naira bilyan 4.7 domin sayen motoci.

6: Su daidaita dangantaka tsakanin su da bangaren gwamnati da kuma jami’an tsaro.

Ana zargin ba su sa-ido a kan Ma’aikatun Gwamnati sosai, sannan kuma akwai zargin ana rika hada baki da su a zangon da ya shude suna amincewa ana nada wadanda ba su cancanta ba a manyan mukamai na gwamnatin tarayya.

Sannan kuma su daidaita mu’amala da jami’an tsaro, ba kamar yadda aka rika rikice-rikice da tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris ba.

8: Su daina azarbabin wanzar da kudirori barkatai ba tare da tantace fa’idojin su ba.

9: Su gaggauta yi wa wasu dokoki kwaskwarima domin magance wasu matsaloli da kasar nan ke ke fama da su. Kamar dokar aikata laifuka a intanet, da aka fi sani da ‘Cybercrime’ ta 2004 da sauran ire-iren su.

10: Su kawo karshen jinkirin mika rahotannin da aka dora wa kwamitoci alhakin yin bincike. Amma dai an yaba wa Majalisa karkashin Bukola Saraki cewa ita ce ta fi saura na baya saurin gabatar da rahotannin da kwamitoci ke gudanar da bincike.

11: SU DAINA FASHIN ZAMAN MAJALISA BA GAIRA BA DALILI

Rahoton da PREMIUM TIMES ta buga cikin 2017 ya nuna ba a fara zaman majalisa sai bayan awa daya da ya kamata a ce an fara. Kuma ana tashi da wuri kamar yadda rahoton ya nuna.

Wasu ‘yan majalisar ba su zuwa sai ranar da suka ga dama, ko kuma ranar da ba su da wani aikin gaban su da ya dame su.

Share.

game da Author