Abin kunya ne a zabi gogarman ‘yan ta-kife Mataimakin Shugaban Majalisa – Ekweremadu

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu, ya bayyana cewa babban abin kunya ne a tarihin Majalisar Dattawan Najeriya a ce gogarman da ya shirya harkallar sace Sandar Mulkin Majalisa ne aka zaba Mataimakin Shugaban ita majalisar.

Ekweremadu, Sanata da Enugu ta Gabas, ya ce ya fito takara ne domin nuna rashin yarda da shigar kutsen da wasu barayi suka yi cikin 2018, har a zaune Majalisa, suka sace Sardar Mulki.

Ya kara da cewa, dama bai yi tunanin zai yi nasara ba, amma dai ya fito ne saboda cin fuskar da aka yi wa majalisa a karkashin jagorancin Sanata Ovie Omo-Agege.

Ekweremadu ya samu kuri’u 37, shi kuma Omo-Agege ya samu 68.

Da ya ke magaba bayan ya fadi zabe, Ekweremadu ya ce bai damu ba don bai yi nasara a kan Omo-Agege ba.

“A ranar da ‘yan takife suka shigo majalisa suka sace Sandar Mulki, ni ne ke jagorantar zaman majalisa. Abin kunya ne a ce gogarman wadannan ’yan takifen ne Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa a yanzu.”

Sannan kuma ya nuna damuwa ganin a lokacin da Omo-Agege ya ja zugar ‘yan takifen, babu abin da aka yi masa, kuma ba a hukunta kowa ba.

Daga nan ya kara da cewa shi dama bai shiga takara don ya yi nasara ba.

Ya shiga takara ce sa’o’i kadan kafin lokacin fara gudanar da zaben a yau a Majalisar Dattawa.

An fara zaben Ekweremadu a Majalisar Dattawa a cikin 2003. Tun daga lokacin ya ke cikin Majalisa har yau.

Cikin 2007 ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, mukamin da ya rike har zuwa makon jiya da ya sauka.
Ya shiga takarar sake zama Mataimaki a yau, inda Sanata Ovie Omo-Agege ya kayar da shi.

Share.

game da Author