A gina mana wuraren haska fina-finan mu ba a jika wasu da kudi ba – Zaharadden ya yi kira ga Gwamnati

0

Fitaccen da wasan finan -finan Hausa sannan kuma Furodusa, Zaharadden Sani ya bayyana cewa kasuwar fina-finan Hausa ruguje yanzu, wahala kawai ake yi ba sana’a da za a samu riba ba.

Zahardden ya fadi haka ne da yake hira da wakilin PREMIUM TIMES ta waya a Abuja inda ya bayyana cewa lallai fa yanzu kawai karfin hali ake yi amma kasuwar fim yayi kasa matuka.

Sannan kuma yayi kira ga gwamnati da kada ta kuskura ta ce za ta bada tallafi ga wasu zababbun aktoci ko masu shirya fina-finai, yana mai cewa idan aka yi haka aljihan su kawai suke cika wa amma ba wai a saka don gyara masana’antar ba.

Zaharaddeen ya kara da cewa maimakon haka gwamnati da kanta ta gina musu wuraren kallo a fadin kasar nan inda kowa zai je ya biya kudi kalilan ya kalli fim.

” Duk tallafin da gwamnati ta bai wa masana’artar fina+fian Hausa a baya ta yaya masana’antar ta amfana da su.

” Ko a yarda ko kada a yarda kasuwar fim ta rushe sannan duk wani dake sana’ar fim ya san da haka. Kamata ya yi mu ba wa gwamnati shawaran yadda za ta samar mana da hanyoyin da za mu yi kudi da fim ba wai gwamnati ta ba mu kudin da za mu kashe ba.

” Ga kasashen duniya nan sun ci gaba sannan mu ina ilimin mu na boko da na Arabiya yake ne da baza mu iya amfani da suba domin tallafa wa kamu. Kawai mun zauna ana ta mana karya.

Ya ce mafita shine gina wuraren kallo wato ‘Cinema’.

” Duk gidan da ka shiga yanzu babu CD domin an daina yayin su. Da zaran an yi haka matasa za su nufi wadannan wurarren kallo da yamma domin rage dare kuma su yi hira tunda sababbin fina-finai sun fito.

Share.

game da Author