A daina kira na ‘Matan Buhari’, akira ni First Lady’, Uwargidan shugaban kasa – Inji Aisha Buhari

0

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bayyana cewa daga yanzu adaina kiran da matan Buhari wato ‘ Wife of the President’ ta ce daga yanzu ta zama uwargidan shugaban kasa ‘ first Lady’.

Aisha ta yi wannan kira ne a taron matan gwamnonin Najeriya in da tace dama can ita ta sa Buhari ya soke ofishin ‘Fist Lady’ din.

” Dama tun farko nine na tilasta wa Buhari kada ya bayyana ofishin ‘First Lady’, ya rika kira na da ‘ matan shugaban kasa’ amma yanzu na yakice wancan shawara, za a rika kira na ne da ‘wannan suna na ‘First Lady’.

Aisha tace ta yi haka ne kuma domin ceto matan gwamnoni da suma ke samun matsala a jihohin su wajen kiran su da matsayin su.

Wannan canji da aka samu dai ya sha bambam da alkawarin da shugaba Buhari ya dauka tun yana yawon kamfen a 2014 inda yayi alkawarin ba zai kirkiro ofishin first lady ba, wato ofishi uwargidan shugaban kasa a lokacin mulkin sa ba.

Buhari da kansa ya ce yin haka saba dokar kasa ce domin dokar bai ce ayi haka ba. Sannan kuma Buharin ya kara da cewa ma’aikatan mata zai kula da ayyukan matan kasar nan, matan sa kuma akira ta da matan shugaban kasa.

Share.

game da Author