Mata ta doka uwar miji a Kotun Magajin Garin Kaduna

0

A safiyar Litinin ne Hadiza Safiyanu mai shekaru 28 ta maka uwar mijinta Aisha Lamido a kotu don ta kira ta karuwa.

Hadiza ta shigar da wannan kara ne a kotun dake Magajin gari a Kaduna.

Hadiza ta bayyana a kotun cewa tun da ta auri mijinta Malam Safiyanu suke zama tare a gidan mahaifiyarsa Aisha a Rigasa.

” Wata rana da misalin karfe 11 na dare ina kwance a daki sai mahaifiyar maigida na Aisha ta shigo dakina ta fara zagina har tana kira na karuwa cewa lalle dole na tattare nawa-i-nawa na bar mata gidanta saboda danta kuma lallai sai ya sake ni.

” Da ban tankata ba sai Aisha ta fita waje ta dauko ice ta rika surfa na da shi yadda kasan na kashe mata da.

Hadiza ta ce duk da wannan duka da Aisha ta yi mata bata bar gidan ba saboda dare ya yi a lokacin amma da garin Allah ya waye sai ta tattara kayanta ta koma gidan kakaninta ta ci gaba da zama.

Ta ce tana rokon kotu da ta tabbatar mata da sakin da Safiyanu ya bata domin ta sami damar kwashe sauran kayanta da suka rage a gidan Aisha.

Ita kuwa Aisha ta musanta aikata haka tana mai cewa lallai Hadiza kazafi ta yi tayi mata.

Alkalin kotun Dahiru Lawal ya dage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Yuni sannan a wannan rana Hadiza za ta gabatar da shaidar sakin da Safiyanu ya yi mata a kotu.

Share.

game da Author