Kungiyar ISWA sun bayyana cewa sune suka kai wa bataliya 158 dake Jihar Barno hari in da yayi sanadiyyar mutuwan sojoji ciki har da kwamandan bataliyan wanda Laftanar Kanal ne.
Idan ba a manta ba a wani harin kare-dangi da Boko Haram suka kai bataliyan sojoji na 158 dake Barno a ranar Alhamis, yayi sanadiyyar mutuwar kwamandan Sojojin Najeriya na wannan bataliya wanda Laftanar Kanal ne.
Bayan sanar wa rundunar sojin Najeriya haka nan take ta tashi dakaru domin su kai dauki wannan sansani.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun arce zuwa kauyen Fuchimiram wanda akalla kilomita 6 yake daga Kareta, a karamar hukumar Mobba.
Wannan mummunar abu ya auku ne a daidai ana bukin ranar dimokradiyya na 12 ga watan Yuni. Sannan kuma wannan hari ya yi daidai da ranar da Boko Haram din suka kai wa sojojin Kamaru hari inda dayawa suka rasu ciki har da mutane akalla 88 kamar yadda suka fadi.
Wannan hari dai yayi munin gaske da ana ganin kila a sake yi wa dakarun Najeriya dake filin daga garambawul sannan kuma an yi musu kasheji da su rika kwana da shiri domin yanzu a lokacin damuna, Boko Haram za su rika kai musu harin bazata.